Trump ya hana masu fama da ƙiba bizar shiga Amurka

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya ƙaddamar da sabon tsarin da zai hana wasu masu neman biza daga ƙasashe daban-daban – ciki har da Nijeriya – samun izinin shiga Amurka idan suna fama da matsananciyar ƙiba ko cututtuka masu alaƙa da ita.

Trump ya bayyana hakan ne a ranar Talata, inda ya ce gwamnati ba za ta ba da ɓisa ga mutanen da lafiyarsu za ta iya zama nauyi ga tsarin kula da lafiya na ƙasar ba.

“Ba za mu hana dukkan masu ƙiba shiga ƙasarmu ba, sai dai waɗanda rashin lafiyarsu zai zama cikas ga tsarin kiwon lafiyar Amurka,” inji Trump a Truth Social.

Shugaban ya bayyana cewa waɗanda suke da ɗan ƙiba za su ci gaba da samun biza, amma waɗanda suka yi girma sosai dole ne su rage ƙiba kafin a amince musu.

Sabon ƙa’idar ta kuma haɗa da tsare-tsaren da za su shafi mazauna ƙasashen waje (eɗpatriates), inda Trump ya bayyana cewa “babu wanda ke da matsananciyar kiba da za a karɓa, ko da kuwa ƙwararre ne.”

“Za mu faɗaɗa wannan doka mu haɗa da mazauna ƙasashen waje. Rosie, ba za ki sake dawowa wannan ƙasa mai girma ba,” inji Trump cikin wani sako mai ɗauke da saƙo kai tsaye ga wata tsohuwar ’yar wasa da ta yi masa suka.

Wannan mataki ya zo ne jim kaɗan bayan sanarwar da Trump ya yi game da sabuwar yarjejeniya da kamfanonin magunguna biyu, domin rage farashin magungunan rage ƙiba kamar Ozempic da Zepbound.

Rahoton jaridar KFF Health News na ranar 4 ga Nuwamba ya bayyana cewa an riga an aika da sabon tsarin zuwa dukkan jakadun Amurka a ƙasashe daban-daban, inda aka umarce su da su dinga duba tarihin lafiya na masu neman visa sosai.

A ƙarƙashin wannan doka, jami’an jakadanci yanzu suna da faɗa a ji wajen ƙin amincewa da neman visa, ba kawai bisa rashin lafiya da ake da ita yanzu ba, har ma da yiwuwar ciyar da kuɗi mai yawa a nan gaba saboda matsalolin lafiya.

Takardar umarnin ta lissafo cututtuka kamar na zuciya da huhu, ciwon daji, ciwon suga da matsalolin kwakwalwa, a matsayin waɗanda ke iya jawo nauyin kashe kuɗi sosai ga gwamnati.

Haka kuma an bayyana kiba a matsayin babban haɗari da ke kawo cututtuka irin su asma, hawan jini da ciwon zuciya — waɗanda ke ƙara tsadar kula da lafiya.

A yanzu jami’an visa suna buƙatar tabbatar da cewa masu neman izini suna da isassun kuɗi don kula da lafiyarsu ba tare da dogaro da taimakon gwamnati ba.

Haka kuma suna duba lafiyar iyalan mai nema – ciki har da yara da tsofaffin iyaye – domin tantance ko nauyin kulawa zai iya zama cikas ga samun kuɗin shiga idan aka ba da biza.

By ukarofi