*Tabbas an yi yunƙurin tumɓuke Akpabio – Sanata Kalu
*Ba haka ba ne, inji Shugaban Masu Rinjaye
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Tsohon Gwamnan Jihar Abia kuma sanata mai wakiltar Abia ta Arewa, Sanata Orji Uzor Kalu, ya tabbatar da cewa labarin yunƙurin tsige Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio.
Ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Majalisar Tarayya, Abuja, inda ya ce an gano makircin tun kafin ya kai matakin da ba za a iya daƙile shi ba.
An ruwaito cewa a lokacin da aka fuskanci yunƙurin wasu daga cikin ‘yan majalisar, an yi gaggawar daƙile lamarin kafin ya tabbata.
Kalu ya ce, duk da kokarin da aka yi na tsige Akpabio, amma haɗin kansu ya taimaka shugaban majalisar ya tsira da kujerarsa.
Ya bayyana cewa, “Duk da an yi yunƙurin tsige shi, amma ba mu bari hakan ta faru ba. Muna aiki tare a matsayin tsintsiya maɗaurinki guda, kuma babu rarrabuwar kawuna. Majalisar Dattawa tana da cikakken goyon baya ga shugabancin Akpabio.”
Ya ƙara da cewa, manyan ‘yan majalisa suna da niyyar ci gaba da tallafa wa gwamnati domin ceto tattalin arzikin ƙasa.
Kalu ya ce, “Matsalolin tattalin arziki sun fi komai muhimmanci a gare mu. Dokokin da muke yi suna da nufin taimaka wa Talakawa, domin mu tabbatar kowa yana da abin ci sau uku a rana.”
Wasu majiyoyi daga cikin Majalisar Dattawa sun bayyana cewa ƙoƙarin tsige Akpabio ya samo asali ne daga wasu ‘yan majalisa da ke jin an ware su wajen raba mukaman kwamitoci.
Haka kuma suna ganin shugabancin majalisa ya ware su a ɓangaren yanke shawara a kan muhimman batutuwa.
Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin ‘yan majalisar jam’iyyar APC da ma na adawa sun yi ƙorafi kan yadda Akpabio ya takaita iko ga ƙungiyar aminansa kaɗan.
Wasu kuma sun nuna rashin jin daɗi a kan yadda ake yanke hukunci a ɓoye, musamman a batutuwan kasafin kuɗi da tsaron ƙasa.
To, sai dai kuma, a wani ƙalubale, Majalisar Dattawan Nijeriya ta ƙaryata rahotannin da ke cewa ana shirin tsige Shugaban Majalisar, Sanata Godswill Akpabio, tana mai bayyana labarin a matsayin ƙarya da ƙoƙarin haifar da ruɗani cikin majalisar.
A zaman majalisar da aka gudanar a Abuja, Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar, Sanata Opeyemi Bamidele, ya bayyana cewa babu wani tattaunawa ko yunƙuri da aka fara domin cire Akpabio daga muƙaminsa.
Ya ce kalaman da ake cewa Sanata Orji Uzor Kalu ya faɗa an fassara su ne ba daidai ba.
“Bayan tattaunawata da Sanata Kalu, ya tabbata cewa maganganun da aka jingina masa an canza su ne daga asalin ma’anarsu,” inji Bamidele.
Sanatan ya gargadi masu yaɗa irin waɗannan bayanai, yana mai cewa hakan na iya karkatar da hankali daga manyan batutuwan da suka shafi al’umma. Ya jaddada cewa dukkan ‘yan majalisa suna nan ɗaya a ƙarƙashin shugabancin Akpabio, tare da daukar “manufofin rashin lamunci ga duk wata hayaniya ko jita-jita.”
“Babu wata tashin hankali a wannan majalisa. Muna da himmar ganin mun kawo sauyi ga rayuwar ‘yan Nijeriya, kuma ba za mu bari jita-jita su kawo mana cikas ba,” inji shi.
A yayin zaman, majalisar ta rubuta wannan bayani a hukumance, inda dattijai suka sake tabbatar da goyon bayansu da amincewa da shugabancin Akpabio. Masu lura da harkokin majalisa sun fassara wannan matsayin a matsayin saƙo kai tsaye ga masu ƙoƙarin kawo rabuwar kai ko rashin kwanciyar hankali cikin majalisar.
Sai dai a wani jawabi daban da ya yi wa manema labarai a Abuja, Sanata Orji Uzor Kalu, wanda ke wakiltar mazabar Abia ta Arewa, ya ce tabbas an yi yunƙurin tsige Akpabio amma ya gaza cimma ruwa.
“Lallai an yi ƙoƙari, amma mun hana hakan. Mun zama iyali ɗaya ne, kuma hakan ba zai faru ba,” inji Kalu.
Tunanin tsige Akpabio ba sabon abu ba ne tun bayan da ya hau mulki a watan Yunin 2023. Sau da dama rahotanni sun ruwaito akwai rashin jituwa tsakanin wasu ‘yan arewa da shugabancinsa, har ma majalisar ta taɓa kaɗa ƙuri’ar amincewa da shi domin nuna goyon baya.
A tsakiyar shekarar 2025 ma, wani sabon rikici ya taso bayan an ce ya samu sabani da Jagoran Majalisa Opeyemi Bamidele game da sanarwar hutun majalisa – abin da ya sake janyo ce-ce-ku-ce kan salon jagorancinsa.
Masana harkokin siyasa na ganin cewa rikicin da ke kewaye da Akpabio ya samo asali ne daga gwagwarmayar iko tsakanin masu biyayya ga fadar shugaban ƙasa da kuma ‘yan majalisa masu neman ‘yancin kansu.
Yayin da magoya bayansa ke ganin kusancinsa da Shugaba Bola Tinubu a matsayin alamar daidaito da kwanciyar hankali, masu suka kuwa suna kallonsa a matsayin alamar cewa majalisar ta rasa cikakken ikon kanta.
