Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Tsohon Shugaban ƙasa, Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa akwai wani lokaci a tarihin Nijeriya da ƙasashen duniya musamman Amurka ke girmama Nijeriya matuƙa, har ba sa ɗaukar muhimmiyar shawara a nahiyar Afirka ba tare da sanar da Abuja ba.
Ya bayyana haka ne ranar Litinin a Abeokuta, Jihar Ogun, yayin taron Presidential Youth Mentorship Retreat (6.0) wanda Cibiyar Ci Gaban Matasa ta Olusegun Obasanjo Presidential Library (OOPL) ta shirya.
Ko da yake Obasanjo bai ambaci sunan shugaban Amurka mai ci yanzu Donald Trump kai tsaye ba, kalamansa na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun saɓani tsakanin ƙasashen biyu sakamakon barazanar Trump na yi wa Nijeriya tasiri ta soji — abin da ake ganin Obasanjo ya yi masa shaguɓe.
“A lokacin da nake Shugaban ƙasa na soja, shugaban Amurka Jimmy Carter ba ya yin wani abu a Afirka ba tare da sanar da mu ba,” inji Obasanjo. “Ba wai suna neman izini ba ne, amma suna sanarwa: ‘Za mu yi kaza.’”
Obasanjo da Carter, wanda ya rasu a watan Disamba 2024, sun kasance abokai na kusanci. Obasanjo ma ya shirya taron tunawa da Carter a Abeokuta domin girmama gudummawarsa ga duniya.
Tsohon shugaban ya koka cewa Nijeriya ta rasa daraja da tasirin da take da shi a fagen duniya bayan samun ‘yancin kai, sai daga baya gwamnatin Muritala–Obasanjo ta dawo da mutuncin ƙasar.
“A lokacin, ƙasashen Amurka sun ga yiwuwar Najeriya ta zama shugabar Afirka. Bayan samun ‘yancin kai, duniya ta ga Nijeriya a matsayin tauraron da ke tashi,” inji shi.
“Amma daga baya muka rasa hakan. Sai da muka dawo da ita lokacin da ni da Muritala muka hau mulki.”
Ya kuma tuna cewa a lokacin mulkinsa, shugabannin Amurka guda uku sun ziyarci Nijeriya — abin da bai sake faruwa ba tun bayan barinsa mulki a 2007.
Obasanjo ya kuma waiwayi rayuwar hafsoshin sojan da suka yi aiki tare da shi a lokacin matashinsu.
“Mun kasance matasa, mun cika da hangen nesa da kishin ƙasa. Ba mu damu da kuɗi ba. Wataƙila mun yi sakaci a wasu lokuta, amma burinmu ba kuɗi ba ne.”
Da yake jawabi kan taken taron “Afirka da Rikice-Rikicen Turai da Gabas ta Tsakiya,” Obasanjo ya kira matasan Afirka da su tashi tsaye su karɓi ragamar mulki daga tsofaffin shugabanni da suka ƙi sauka daga kujeru.
Ya kawo misali da zaben Kamaru inda shugaban ƙasar Paul Biya, mai shekara 92, ke neman ci gaba da mulki. “Ku ne shugabannin yau, ba na gobe ba. Idan kuka bar gobe ga shugabannin yau, za su lalata makomarku,” inji shi. “Dole ne ku zama masu kawo canji mai amfani — idan ba haka ba, ba za ku sami matsayi ba.”
Ya kuma jaddada cewa matasa su yi amfani da yawan su wajen canja lamura, “Lambar ba ta da ma’ana sai idan kuka yi amfani da ita wajen samun fa’ida,” inji shi.
Sai dai ya nuna damuwa cewa wasu matasan da suka samu muƙamai a gwamnati ba su tabbatar da tsammanin cewa matasa ne ke kawo sabon haske ba.
