Gwamnatin Nijeriya ta soke amfani da harsunan gida wajen koyarwa a makarantu

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya  ta umurci malamai a faɗin Nijeriya da su ci gaba da amfani da harshen Turanci a matsayin harshen koyarwa a makarantu, lamarin da ke nuna cewa shirin da aka yi na koyarwa da harsunan gida bai samu karɓuwa ba.

Ministan Ilimi, Dekta Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan yayin wani taron ƙasa da ƙasa kan Harshen Ilimi na 2025, wanda Majalisar Burtaniya ta shirya a birnin Abuja. A cewar ministan, wannan matakin na gwamnati ya biyo bayan buƙatar da ta taso ta inganta koyo da kuma tabbatar da daidaito a tsarin koyarwa a duk faɗin ƙasar.

Taron ya tattaro ƙwararru daga sassa daban-daban ciki har da masana, masu tsara manufofi, masana ilimi, masu bincike da abokan hulɗa daga Afirka, Kudancin Asiya da Birtaniya domin tattauna hanyoyin inganta koyo ta amfani da harshe.

Dekta Alausa ya jaddada cewa duk da muhimmancin kiyaye harsunan asali wajen tabbatar da al’adunmu, Turanci ne ya kamata ya ci gaba da zama harshen koyarwa tun daga matakin firamare har zuwa makarantu na gaba da sakandare.

Ya ce, hakan zai taimaka wajen inganta fahimtar ɗalibai da kuma daidaita gogayyar ilimi tsakanin ɗaliban Nijeriya da takwarorinsu na sauran ƙasashe.

By ukarofi