
Nijeriya ta kai zagayen ƙarshe a wasan neman gurbin shiga gasar kofin duniya, bayan da ta doke Gabon da ci 4 da 1 a birnin Rabat a Morocco.
Akor Adams ne ya fara ci wa Super Eagles ƙwallo a minti na 78 daga baya Gabon ta farke ta hannun Mario Lemina dab a tashi daga fafatawar.
Sun tashi 1-1 a minti 90 da suka buga, hakan ya sa aka yi karin minti 30.
Da suka koma cigaba da fafatawar ne sai Super Eagles ta ƙara na biyu ta hannun Chidera Ejuke, sannan Victor Osimhen ya ƙara na biyu da na uku.
A yanzu haka dai Super Eagles za ta kara da ƙasar Jamhuriyar Dimukraɗiyyar Kongo a wasan ƙarshe na cike gurbin, wadda ta doke Kamaru a karawarsu ta jiya Alhamis.
Kenan, wadda ta yi nasara daga Afirka za a haɗa ta da Bolivia (CONMEBOL) da New Caledonia (OFC) tare da wata daga Asiya da Concacaf a wasannin cike gurbi tsakanin tawaga shida da za su kara daga ranar 23 zuwa 31 Maris 2026.
Daga nan za a samu biyun da za su cike gurbin tawaga 48 da za su fafata a birane 16 tsakanin Amurka da Canada da kuma Mexico da za a fara daga 11 ga watan Yuli zuwa 19 ga watan Yuli.
