
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
An samu tabbacin Super Eagles ta Nijeriya za ta kara da Jamhuriyar Dimukraɗiyyar Kongo a wasan ƙarshe na neman cike gurbin gasar Kofin Duniya.
Za a buga wasan ne a Birnin Rabat na ƙasar Moroko, a ranar 17 ga watan Nuwamba, 2025.

Hakan na zuwa ne bayan da Kongo ta doke Kamaru da ci 1-0 a wasan kusa da na ƙarshe, yayin da ita kuma Super Eagles ɗin ta lallasa Gabon da ci 4 da 1 a lokacin kararwarsu na zango na biyu na ƙarin lokaci.
Ɗan wasa Victor Osimhen ne ya zura ƙwallaye biyu a zangon bayan Akor Adams da Chidera Ejuka sun fara zura guda-guda.
A yanzu duk wanda ya yi nasara tsakanin Kongo da Nijeriya, zai haɗu da abokan karawa daga nahiyoyin Asiya da Oceanic.
