Matasa sun kai ziyarar jaje da goyon baya ga Sanata Abdullahi Adamu da Sarkin Keffi

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Keffi

Wata tawaga ta matasa masu ruwa da tsaki daga mazaɓar Nasarawa ta Yamma a Jihar Nasarawa, tare da jagorancin kwamishinan lafiya na jihar, Dokta Gaza Gwamna, sun kai ziyarar ban-girma ga Sanata Abdullahi Adamu, Turakin Keffi, a gidansa da ke Keffi.

Ziyarar na da manufar nuna goyon baya da jaje game da gangamin da ake yi na ganin an miƙa kujerar gwamnan Jihar Nasarawa zuwa Nasarawa ta Yamma.

Matasan, waɗanda suka fito daga ƙananan hukumomi biyar wato Keffi, Karu, Kokona, Nasarawa da Toto sun gode wa Sanata Adamu bisa kishin ƙasa, jarumta da jajircewarsa wajen ganin an samu adalci, daidaito, da cikakken wakilci a tsarin shugabancin jihar.

Dokta Gwamna ya jaddada buƙatar haɗin kai tsakanin matasa, yana mai cewa batun tsarin rabon mulki (zoning) ya wuce son rai ko bambancin jam’iyya, domin yana da alaƙa da adalci da shigar kowa cikin tafiyar siyasar Jihar Nasarawa.

Tawagar ta kuma kai ziyarar ban-girma ga Mai Martaba Sarkin Keffi, Dakta Chindo Yamusa III, a fadarsa. Dakta Gwamna ya roƙi Mai Martaba ya bayar da cikakken goyon baya da tasirin sarauta wajen tabbatar da an sauya kujerar gwamna zuwa Nasarawa ta Yamma.

Sarkin ya yaba wa matasan bisa salo na lumana da mahanga ta siyasa da suka nuna, yana ƙarfafa musu gwiwa da su ci gaba da zama masu haɗin kai tare da kare adalci cikin yanayin zaman lafiya, tattaunawa da girmama hukuma.

Shugaban tawagar ya yi godiya ga Sanata Adamu da Sarkin Keffi bisa karɓa da goyon baya.

Kwamared Ja’afar Loko, sakataren kwamitin ƙanana kuma shugaban kwamitin shirya taron, ya tabbatar da shirin matasan na yin babban gangamin wayar da kai da samun goyon bayan jama’a a faɗin jihar domin ganin an cimma burin tsarin rabon mulki.

“Batun rabon mulki ya wuce son rai ko jam’iyya; yana da nasaba da adalci da shigar kowa a jihar Nasarawa.”

“Za mu ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki, dattawa, gargajiya da shugabannin siyasa domin bunƙasa zaman lafiya da hadin kai yayin da muke bin wannan muhimmin buri.” – Inji shi.

Ziyarar ta samu halartar muhimman matasa masu ruwa da tsaki daga dukkan mazaɓu 59 na yankin, ciki har da kwamishinoni na jiha, ‘yan majalisar dokoki, da shugabannin ƙananan hukumomi.

By ukarofi