
Ma’aikatar Tsaro da Harkokin Cikin Gida ta Jihar Kaduna ta ƙaryata wani rahoton bogi da jaridar SaharaReporters ta wallafa, wanda ke ikirarin cewa babu ko sisin kwabo da aka kashe a ɓangaren tsaro a jihar.
A cewar ma’aikatar tsaron wannan rahoto ƙarya ne kuma an wallafa shi ne da gangan domin yaudarar jama’a tana mai cewa gwamnatin Malam Uba Sani ta dade tana bai wa tsaro muhimmanci ta hanyar zuba jari mai yawa a fannin fasahar sa ido, kayan aiki, motocin aiki da kuma karfafa leƙen asirin al’umma wadanda suka kai darajar biliyoyin naira.
A wata sanarwa da kwamishinan ma’aikatar tsaron, Barista Sule Shu’aibu ( SAN) ya fitar ya ce daga cikin sabbin matakan tsaro da aka dauka akwai tura sabbin sansanonin Forward Operating Bases, motocin Hilux guda 150, da babura 500 domin karfafa yaki da ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane.
Yace ma’aikatar ta sake tabbatar da kudirin Gwamna Uba Sani na ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a, tare da kira ga kafafen yada labarai su rika tabbatar da sahihanci da adalci a rahotanninsu.
