Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta ƙasa (NAFDAC) ta bayyana shirinta na ɗaukar ƙarin ma’aikata 1,000 domin ƙarfafa ikon gudanar da aiki da kuma aiwatar da haramcin haɗawa da sayar da barasa a cikin leda da ƙananan kwalabe ƙasa da mililita 200.
Shugabar hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye, ce ta bayyana hakan a ranar Talata yayin ganawa da manema labarai a Abuja.
Farfesa Adeyeye ta sake jaddada cewa an haramta haɗawa, sayarwa, da rarraba giya da aka haɗa a cikin leda da kwalabe ƙanana, bisa matsayar da Majalisar Dattawa ta yanke da kuma umarnin Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya.
“Wannan mataki mai ƙarfi yana nuna nauyin da ke kanmu na kare lafiyar ‘yan Nijeriya daga haɗurran da barasa maras ƙa’ida ke haddasawa, musamman ga yara, matasa da matan da ke kan hanyar girma,” inji ta.
Ta bayyana cewa waɗannan giya da ake sakawa a ƙananan leda ko kwalabe suna da sauƙin samu da sauƙin ɓoyewa, wanda hakan ke haifar da yawaitar amfani mara tsari da jaraba, musamman tsakanin yara da direbobi.
Farfesa Adeyeye ta kuma nuna damuwa da yadda barasa mai ƙarfi a ƙaramar leda ke zama barazana ga lafiyar jama’a da kuma harkar tsaro, kasancewar yawan matasa na fara shan giya tun da wuri, wanda ke kai su ga shaye-shaye da aikata laifuka.
“Wannan matsalar lafiyar jama’a na da alaƙa da tashin hankali a gida, haɗurran hanya, barin makaranta da sauran munanan ɗabi’u,” inji ta.
Ta ce, wannan haramci na da manufa ta kariya ne, ba horo ba, kuma ya dogara da shaidar kimiyya da ƙa’idojin duniya.
“Mun yanke wannan shawara ne domin kare lafiyar matasan Nijeriya da makomar ƙasar. Ba za mu ci gaba da sayar da lafiyar al’umma don amfanin tattalin arziki na ɗan lokaci ba,” ta ƙara da cewa.
Ta kuma bayyana cewa dokar ba ta shafi duka nau’in giya ba, sai dai giya mai ƙarfi da aka sa a leda ko ƙaramin kwalba ƙasa da milimita200.
Farfesa Adeyeye ta jaddada cewa matakin Majalisar Dattawa ya yi daidai da yarjejeniyar da aka cimma a baya da kuma alƙawarin Nijeriya ga shirin WHO na rage amfani da barasa (WHA63.13, 2010).
