Gasar Kofin Duniya ta 2026 ita ce ta ƙarshe da zan buga – Ronaldo

Spread the love

Dan wasan tawagar Portugal, Cristiano Ronaldo, ya tabbatar cewa Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026, ita ce ta ƙarshe a rayuwarsa ta tamaula da zai halarta.

Mai shekaru 40, wanda ya ci ƙwallo 953 a matakin ungiyoyi da ƙasa, ya kuma ce zai yi ritaya kaka ɗaya ko kuma biyu nan gaba.

Gasar Kofin Duniya ta badi, wadda za a gudanar a Amurka da Canada da Meɗico, za ta kasance ta shida da Ronaldo zai halarta.

Ronaldo, tsohon ɗan wasan Manchester United da Real Madrid da Juventus, wanda ke wasa a Al-Nassr ta Saudi Arabia, ya ci ƙwallo 143 a tawagar Portugal, shi ne kan gaba a wannan bajintar, yanzu yana son cimma burin zura ƙwallo 1,000 a dukkan wasannin da ya buga a tarihi.

Ronaldo ya taimaka wa Portugal ta lashe gasar nahiyar Turai ta Euro 2016, amma Kofin Duniya na daga cikin babban kofin da bai taɓa lashewa ba — duk da cewa ya karɓi kyautar Ballon d’Or biyar.

Tawagar da Roberto Martinez ke jan ragama, ba ta samu gurbin shiga gasar kofin duniya ba da za a yi a baɗj, amma da zarar ta doke Jamhuriyar Ireland ranar Alhamis za ta samu tikitin.

By ukarofi