Guardiola ya ja ragamar wasanni 1,000 a Man City

Spread the love

Kocin Manchester City, Pep Guardiala ya ja ragamar wasanni a 1,000 a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester City.

Ya cika na 1,000 ne a Man City ta doke Liverpool 3-0 a wasan mako na 11 a gasar Premier League da suka fafata a Etihad ranar Lahadin da ta gabata.

Man City ta fara cin ƙwallo ta hannun Erling Haaland a minti na 29 daga baya Nico Gonzalez ya ci na biyu, sai kuma Jeremy Doku ya kara na uku.

Karo na 14 da Haaland ya zura ƙwallo a raga daga karawa 11 a Premier League a kakar nan – karo na biyu da ya yi wannan ƙwazon, bayan cin 17 a wasa 11 a babbar gasar tamaula ta Ingila a 2022/23.

Man City ta koma mataki na biyu a kan teburi da maki 22 da tazarar huɗu tsakani da Arsenal mai jan ragama.

Ita kuwa Liverpool wadda karo na biyar ta yi rashin nasara a Lig a kakar nan tana da maki 18 ta yi kasa zuwa mataki na takwas.

Shi ne wasa na 1,000 da Pep Guardiola ya ja ragama tun daga lokacin da ya fara aikin kociyan tamaula daga karamar ƙungiyar Barcelona zuwa babbar da Bayern Munich da kuma Manchester City.

Kenan ɗan ƙasar Sifaniya, mai shekara 54, ya yi nasara ta 715 kenan daga ciki aka doke shi karo 128.

By ukarofi