Gwamnan Taraba zai koma APC

Spread the love

Gwamnan Jihar Taraba ya kammala shirye-shiryen ficewa daga jam’iyyar PDP zuwa mai mulki, wato APC.

Hakan na zuwa ne bayan dogon nazari da tattaunawa tsakanin manyan jagororin siyasa a jihar da matakin na ƙasa.

Majiyoyi masu ƙarfi sun tabbatar da cewa an sanya ranar 19 ga wannan watan domin gudanar da bikin tarbarsa cikin jam’iyyar ta APC a wani babban taro da ake sa ran zai janyo hankalin jam’iyyu da dama a faɗin ƙasar.

Ana sa ran zuwan gwamnan cikin APC zai kawo sabon salo a tsarin siyasar Taraba tare da yiwuwar samun sauye-sauye a a harkokin ci-gaban siyasar gwamnan.

By Babaji