Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
A mataki na tabbatar da ingantacciyar kula da lafiyar al’umma, shugaban ƙaramar hukumar Katsina, Hon. Isah Miqdad AD Saude, ya ƙaddamar da aikin gina asibitin yara da mata masu juna biyu a mazaɓar Wakilin Arewa A.
Shugaban wanda ya sami wakilcin shugaban majalisar kansilolin ƙaramar hukumar Katsina, Hon. Ishaq Tasi’u Modoji, ya bayyana cewa aikin gina wannan asibiti na daga cikin manufofin gwamnatin ƙaramar hukumar wajen sauƙaƙa wa mata masu juna biyu da ƙananan yara wajen samun kulawar lafiya a kusa da su ba tare da dogon tafiye-tafiye ba.
Shima kansilan mazabar wakilin Arewa A, Hon. Kamaladeen Mamman, ya yabawa shugaban ƙaramar hukumar bisa amsa koken jama’ar mazaɓar wajen gina asibitin da suka daɗe suna fatansa.
Babu shakka yanzu al’umma mazaɓar ba sai sunyi dogon tafiya ba kafin duba lafiyar su.
Taron ya samu halartar masu ruwa da tsaki na mazaɓar da shugabannin al’umma, waɗanda suka bayyana farin cikinsu da wannan aikin alheri da ke nuna irin jajircewar gwamnatin ƙaramar hukumar Katsina wajen inganta harkokin kiwon lafiya a matakin farko.
