JIBWIBS a Katsina ta ƙalubalanci naɗin sabon shugaban hukumar zaɓe na ƙasa

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

A wata takardar sanarwa ɗauke da sa hannun shugaban ƙungiyar Izalatul bidi’a wa Ikamatul sunnah reshen jihar Katsina Sheikh Yakubu Musa Hassan Sauttus sunnah ya sanya hannu, ƙungiyar ta nuna mamaki da damuwa dangane da naɗin Farfesa Amupitan Joash.

Sanarwar ta ce ƙungiyar ta nuna kaɗuwar ta akan naɗin saboda maganganu marasa tushe da makama da yayi a shekarar 2020 inda ya gabatar da wata ƙasida da ya buga mai taken “LEGAL BRIEF”.

Sheikh Yakubu Musa ya bayyana cewa Farfesa Joash yayi zarge zarge marasa tushe da suka ƙasƙantar da cin mutuncin Musulmin ƙasar.

Ya ƙara da cewa Sabon shugaban hukumar zaɓen ya kuma zargi Musulmin ƙasar da kisan kiyashi ga Kiristoci a ƙasa,zargin da bashi da tushe balle makama.

Duk dai rubutun nasa Amputin ya yi zargin cewa jihadin Usman Danfodiyo anyi shine domin ƙirƙirar Boko Haram da satar mutane wanda Sheikh Yakubu Musa ya musanta haka.

“Masana tarihi sun tabbatar da cewa jihadin Usman Danfodiyo anyi ne domin ilmantar da Musulmi da tabbatar da anyi gaskiya da adalci a tsakanin al’umma ba ƙirƙirar ta’addanci ba,”inji Sheikh Musa Hassan.

Shugaban JIBWIBS ya ce rashin mutunci na ƙarshe da Amputin ya yi shine lokacin da ya nema ƙasashen duniya su kawo wa Kiristocin Nijeriya ɗauki dangane da kisan kiyashin da Musulmi suka aikata wanda wannan kalamai nasa da yayi barazana ne ga tsaron ƙasa,”Inji Musa Hassan.

“Tun shekaru biyar kenan da suka wuce sabon shugaban hukumar zaɓen ya ke rubuce-rubuce na ƙiyayya ga Musulmi da nuna ɓangaranci, mu ke ganin a matsayin sa na shugaban hukumar zaɓe ba zai yi adalci a zaɓe mai zuwa ba,”inji Sheikh Yakubu Musa.

Ya ce duk da rubutun da yayi mai taken “LEGAL BRIEF” wasu ƙungiyoyi masu zaman kansu da ke mara masa baya na kiran ƙasar Amurika da ƙaƙabawa Nijeriya takunkumi,wasu ma yan majalisar ƙasar Amurka ta kai ga suna neman shugaban ƙasar, Donald Trump da ya kawowa kasar Nijeriya hari domin kare Kiristoci daga kisan kiyashi a hannun Musulmi.

Sai dai ƙungiyoyi masu zaman kansu da ke mara masa baya sun shawarci shugaban hukumar zaɓen da ya yi adalci da nuna kowa nashi ne wajen gudanar da zaɓe inji shugaban JIBWIBS.

Sai dai Sheikh Yakubu Musa ya bayyana cewa Farfesa Amputin da yake da mugun manufa ga Musulmi bai kamata ya jagoranci gudanar da zaɓe ba.

JIBWIBS ta ce ta na mamakin yadda wannan Farfesa mai zurfin ilimi ke neman wata ƙasa ta kakabawa mahaifarsa takunkumi,har ma sojoji su kawo wa Nijeriya hari,”inji Sautus Sunnah.

Akan haka JIBWIBS ta yi mamakin yadda aka ba wannan mutumin mai mugun manufa shugaban hukumar zaɓe.

Akan wannan ne JIBWIBS ta shawarci Farfesa Amputin cikin mutunci da ajiye aikin sa,idan kuma bai ajiye ba ƙungiyar ta buƙaci shugaban ƙasa Bola Tinubu da gaggauta cire shi daga muƙamin sa, ɗaukan wannan mataki zai ba Musulmi ba ma na Nijeriya ba har ma da duniya baki ɗaya samun natsuwa.

Ƙungiyar ta ce wannan mataki da ta ɗauka bashi da nasaba da siyasa ko muryar ‘yan adawar siyasa sai domin neman kariya da a yiwa Musulmi adalci domin samun zaman lafiya a ƙasar.

Sheikh Yakubu Musa Hassan ya ce hukumar zaɓe na buƙatar shugaba da zai riƙe gaskiya da adalci ba wanda zai kawo rarrabuwar Kawuna ba.

By ukarofi