
Rikici ya ɓarke a hedikwatar jam’iyyar PDP da ke Abuja, wanda ya tilasta wa ƴan sanda harba hayaƙi mai sa hawaye domin tarwatsa magoya bayan jam’iyyar a daidai lokacin da ake cigaba da taƙaddama akan shugabancin jam’iyyar tsakanin bangarorin da ke hamayya da juna.
Rikicin ya ɓarke ne a Wadata Plaza yayin da Gwamna Seyi Makinde, Bala Mohammed, da shugabannin jam’iyyar da Turaki ke jagoranta suka isa.
Al’amarin ya haifar da rikici da ‘yan sanda da magoya bayan ɓangaren Sanata Anyanwu waɗanda suka yi ƙoƙarin hana shiga farfajiyar sakatariyar.
Ministan Abuja, Nyesom Wike, shi ma ya isa Wadata Plaza amma har yanzu bai sauka daga motarsa ba, inda ya shafe sama da mintuna 30 a cikin motar.
A halin yanzu, Gwamna Seyi Makinde da Bala Mohammed suna nan a harabar.
Gwamnonin biyu sun yi wa ‘yan jarida bayani, inda suka bada labarin abinda ya faru, ciki har da hayaki mai sa hawaye da ‘yan sanda suka harba da kuma turjiya da suka fuskanta daga magoya bayan ɓangaren Sanata Anyanwu.
