
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnatin Jihar Katsina ta shirya zama tsakanin kwamitin malaman addini da Malam Yahaya Masussuka biyo bayan wasu zarge-zarge da ƙorafe-ƙorafe da wasu malamai a jihar suka yi cewa salon wa’azinsa ya saɓa wa ka’idojin shari’ar Musulunci.
Bayanin haka na ƙunshe a wata sanarwa da ta fito daga ofishin Sakataren Gwamnatin jihar wanda daraktan Yaɗa Labarai, Ibrahim Alamu Gafai ya sanya wa hannu a yau Talata.
A cewar sanarwar, Malam Yahaya a kwanakin baya ya kai korafi cewa wasu mambobin ƙungiyar Izala na zaginsa tare da yi masa barazana, inda gwamnati ta mika batun zuwa ga Majalisar Masarautar Katsina, karkashin jagorancin Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman.
Sanarwar ta cigaba da cewa, Sarkin ya gudanar da zaman sulhu a fadarsa tare da gayyatar Malam Yahaya da wasu malamai, inda Sarkin ya ja hankali kan cewa ba a amince a gudanar da wa’azi cikin salon da zai kawo rikici ko zubar da mutunci ba, inda sanarwar ta ƙara da cewa duk da wannan mataki da Masarautar ta ɗauka, gwamnati har yanzu tana samun bayanai cewa taƙaddama na ƙara ta’azzara a tsakaninsa da ƴan ƙungiyar Izala a jihar.
A saboda haka ne gwamnan jihar, Malam Dikko Raɗɗa ya umarci Malam Yahaya da ya bayyana a gaban kwamitin
malaman domin kare kansa a kan zarge-zargen da ake yi masa.
Kazalika, kwamitin da gwamnatin ta kafa zai tsara dokoki da ƙa’idojin gudanar da wa’azi da karantarwa a faɗin jihar, tare da ɗaukar mataki kan duk wanda ya karya tsarin, a yayin da gwamnati ke yin kira ga al’umma da su kwantar da hankalinsu, tana mai tabbatar da cewa za a gudanar da zaman bisa gaskiya da adalci.
Su dai ƴan Izala suna zargin Malam Masussuka mai aƙidar Ƙur’ani zalla, da gudanar da wa’azi a baibai da ya saɓa wa addinin Musulunci.
