
Mai Shari’a James Omotosho na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ya yanke wa Nnamdi Kanu hukuncin ɗaurin rai da rai bayan da masu gabatar da ƙara suka tabbatar da tuhume-tuhumen da ake yi masa.
Tuhume-tuhumen da aka yi wa Kanu sun haɗa da ta’addanci da tunzura jama’a su kashe ƴan sanda da tayar da zaune-tsaye.
Haka kuma, ya yanke masa hukuncin zaman gidan kurkuku na tsawon shekaru 20 da shekaru biyar na laifuka bakwai ba tare da zaɓin biyan tara ba.
Hakan na zuwa ne bayan tsawon lokaci ana tsare da jagoran na ƴan ƙungiyar fafutukar kafa ƙasar Biafaran (IPOB).
