Jihar Taraba ta rufe dukkan makarantun kwana sakamakon ƙaruwar matsalar tsaro

Spread the love

 Daga WAKILINMU

A wani mataki na samar da tsaro ga ɗaliban Jihar Taraba, Gwamnatin Jihar ta ba da umarnin rufe dukkan makarantun kwana dake ƙarƙashin gwamnati da masu zaman kansu a cikin jihar, ba tare da ɓata lokaci ba.

Umarnin na zuwa ne a cikin wata sanarwa da gwamnati ta fitar ranar Asabar 22 ga watan Nuwamba, 2025 a garin Jalingo, biyo bayan ƙaruwar fargaba kan taɓarɓarewar tsaro a wasu sassan ƙasar nan, musamman game da garkuwa da ɗaliban makarantu da aka yi a jihohin Kebbi da Neja.

Gwamnati ta ɗauki wannan mataki ne, a cewar sanarwar, sakamakon rahoton jami’an tsaro game da yadda rayuwar ɗaliban makarantun kwana ke cikin yiwuwar fuskantar haɗari a jihar.

Sanarwar mai ɗauke da sa hannun Kwamishinar Ma’aikatar Kula da Ilimin Ƙananan Makarantu a Jihar Taraba, Dr. Augustina Godwin, ta ƙara bayyana cewa Gwamnan jihar Agbu Kefas, ya ba da wannan umarni ne saboda kare rayuwar ɗaliban jihar daga duk wani harin ýan ta’adda.

Kwamishinar ta ce lura da halin da ake ciki dukkan ɗaliban jihar da ke makarantun kwana za su koma zuwa ɗaukar karatu daga gida, har sai abin da hali ya yi.

 Sanarwar ta buƙaci dukkan shugabannin makarantun sakandire na kwana a jihar su sallami ɗaliban su su koma gida, ba tare da ɓata lokaci ba.

A wani rahoto makamancin wannan, Babban Sakataren Hukumar Kula Da Makarantun Gaba da Firamare ta Jihar Taraba, cikin wata sanarwa da aka yaɗa ta a jihar, ya umarci shugabannin ƙungiyoyin makarantu masu zaman kansu na APSON da NAPPS, da lallai su yi biyayya ga wannan umarni na gwamnati, su rufe dukkan makarantun kwana da suke da su.

By ukarofi