Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kumgiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF) ta yi kira mai ƙarfi ga al’ummar Arewacin Nijeriya da su yi amfani da damar da ake da ita yanzu ta yin rajistar katin zaɓe, domin shiryawa babban zaɓen 2027.
Kiran na zuwa ne a lokacin da ake samun ƙarancin kulawa daga jama’a game da rajistar da ake gudanarwa a sassan ƙasa.
Yayin ƙaddamar da shugabannin ƙananan hukumomi 27 na ACF a garin Dutse, shugaban ƙungiyar na jihar Jigawa, Aminu Dalhatu, ya nuna takaicinsa kan yadda yankin Arewa ya yi baya a fannin ilimi, lamarin da ya ƙara jefa shi cikin dogon giɓi na ci gaban ƙasa.
Ya ce wannan koma-baya na tasiri matuƙa wajen rage yawan mutanen da ke shiga harkokin zaɓe da gudanar da al’amuran dimokuraɗiyya.
ACF ta bayyana damuwarta kan yadda ake samun gazawar jama’a wajen fitowa domin yin rajista, musamman a Jigawa, inda rahotanni ke nuna cewa halartar jama’a ya yi kadan sosai idan aka kwatanta da yawan waɗanda suka cancanci yin rajista.
Shugaban ya ce, wajibi ne ‘yan Arewa su farka daga sakaci, su kare muradun yankinsu ta hanyar fitowa cikin yawan jama’a don yin rajista da kuma tabbatar da cewa ƙuri’unsu ba su ɓata ba.
Dalhatu ya jaddada cewa shekaru huɗu da suka gabata sun kawo canje-canje da dama a cikin al’umma — wasu sun kai shekarun da ake iya yin zaɓe, wasu kuma sun yi ƙaura daga wani yanki zuwa wani. Don haka ya ce ya zama dole mutane su sabunta rajistarsu ko su yi ta farko idan ba su yi ba.
Ya kuma yi kira ga hukumomi da ƙungiyoyi su ƙara faɗakar da jama’a domin a samu ƙarin tasiri, yana mai cewa ACF za ta ci gaba da taka rawar gani wajen tallafawa duk wani yunƙuri na gwamnati da zai ƙarfafa dimokuraɗiyya.
