Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Babban Kwanturola-Janar na Hukumar Kwastom ta ƙasa (NCS), Bashir Adewale Adeniyi, ya bayyana cewa babban taron Kwastom da Haɗin Gwiwar Afirka a Harkokin Cinikayya (C-PACT) da aka gudanar a Abuja ranar Litinin, 17 ga Nuwamba 2025, zai taka muhimmiyar rawa wajen hanzarta farfaɗowar tattalin arziƙin Nijeriya da faɗaɗa damar fitar da kayayyaki na ƙananan masana’antu ƙarƙashin tsarin AfCFTA.
Da yake zantawa da manema labarai a Fadar Shugaban ƙasa, Adeniyi ya ce, cikakken goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ga taron ya nuna muhimmancin da gwamnatin ke bai wa harkar cinikayyar cikin gida.
A cewar Adeniyi, sama da hukumar kwastom 30 daga ƙasashen Afrika sun halarci taron, ciki har da wakilai a matakin Darakta-Janar daga ƙasashe 22, tare da manyan jami’an gwamnati, ‘yan kasuwa, masana’antu, kamfanonin jiragen sama da na ruwa, ma’aikatan tashoshin jiragen ruwa da hukumomin sufuri.
Ya ce, taron zai mai da hankali kan rushe manyan shingayen da ake fuskanta a cinikayyar Afrika, tare da zurfafa haɗin kai tsakanin ƙasashen nahiyar.
“Wannan taro wata sanarwa ce daga Nijeriya ake yi ga nahiyar Afrika cewa muna shirye don sabon babi na tattalin arziƙi. AfCFTA na ɗauke da damar da za su canja mana tarihi,” inji shi.
Adeniyi ya ce, saɓanin tsohuwar al’ada, wannan karo ‘yan kasuwa za su buɗe taron domin su bayyana kai tsaye wa shugabannin kwastom matsalolin da ke hana cinikayya gudana cikin sauƙi — daga cikas na takardu zuwa tsaiko a tashoshi.
A cewarsa, cinikayya bata hannun gwamnati take ba, domin masu kayayyaki ne ke aiwatar da ita, don haka dole a saurari muradunsu a tsarin gyare-gyare.
Ya jaddada cewa cinikayyar cikin Afrika na daga cikin manyan injunan da ba a yi amfani da su yadda ya kamata ba. Duk da cewa Nijeriya ta samu ƙarin sama da kashi 30 a fitar da kayayyaki cikin shekaru biyu, yawancin kayayyakin ba su nufi ƙasashen Afrika ba.
Adeniyi ya ce, karkatar da kasuwancin zuwa kasuwar Afrika mai darajar dala tiriliyan 3.4 zai rage tsadar sufuri, ya ƙara darajar kayayyaki, ya kuma buɗe sababbin harkokin masana’antu da ayyukan yi.
Ya ambaci nasarorin da aka riga aka samu a tsarin Authorized Economic Operator (AEO) inda ƙananan masana’antu ke fitar da kayan fata, kayayyakin hannu, abinci da furannin zogale zuwa Kudancin Afrika—abin da ke tabbatar da cewa Nijeriya na da cikakkiyar kwarewar yin gogayya cikin nahiyar.
Ya danganta shirin ƙasa na AfCFTA da sauye-sauyen gwamnatin Tinubu, ciki har da modernization, rage cunkoso a tashoshi, inganta kayayyakin more rayuwa, da kafa National Single Window.
Adeniyi ya ce, karɓar baƙuncin da Nijeriya ta yi na Kasuwar Duniyar ta Afrika ‘Intra-African Trade Fair’, da matsayin da Shugaba Tinubu ya samu na Gwarzon Kasuwancin Afrika ‘Champion of Intra-African Trade in Services’, ya ƙara ƙarfafa matsayin ƙasar.
Dangane da damuwar rasa kuɗaɗen shiga saboda sassauta haraji, Adeniyi ya ce, “Haƙiƙa muna tattara kuɗaɗen shiga, amma cinikayya ce ke kawo wadata. Ba za ka ci kekinka ka ajiye shi ba.”
Ya bayyana muhimman sakamakon da Nijeriya ke son cimmawa—ciki har da matsaya guda ta kwastom a kan AfCFTA, warware cikas na rashin haraji, haɗa kwastom da bankuna da ‘yan kasuwa a dandali guda, da kuma ƙarfafa haɗin kai da Afreɗimbank da Ma’aikatar AfCFTA.
Adeniyi ya nuna cewa aiwatar da AfCFTA na daga cikin KPIs da aka ɗaura wa jagorancinsa, yana mai cewa aiwatar da shirin na buƙatar juriya, horo da ƙarfi na siyasa.
Ya kuma bayyana cewa sabon tsarin CIPAC ya haɗa manyan hukumomi kamar NEPC, NEɗIM, bankunan kasuwanci da NPA, domin goyon bayan rawar jagorancin Kwastom.
Ya tuna da ƙalubalen da ƙungiyoyin yankuna suka taɓa fuskanta, yana mai cewa matsalolin na nahiyar baki ɗaya ne, ba Nijeriya kaɗai ba.
A ƙarshe, ya ce hukumar kwastom ta samu ƙaruwar kuɗaɗen shiga sama da kashi 70 cikin 2023, da kashi 101 cikin 2024, kuma a bana ana sa ran tarihi zai sake kafuwa.
Adeniyi ya tabbatar da cewa hukumar Kwastom na nan daram kan manyan nauyinta: kafa tsaro, tara kuɗaɗen shiga, da sauƙaƙa cinikayya a Nijeriya.
