Cin ganda yana barazana ga masana’antar fata ta Nijeriya, inji Gwamnatin Tarayya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayya ta yi gargaɗi kan yadda ci gaba da cin fatar shanu, wato ganda, wanda wasu ƙabilu suka fi sani da komo, ke barazana ga ɗumbin arzikin masana’antar fata a Nijeriya, wadda darajarta ta kai kimanin dala biliyan biyar.

Wannan gargaɗin ya zo ne yayin ƙaddamar da ‘Yaƙin ƙasa Kan Cin Ganda’ da aka gudanar a Abuja a ranar Alhamis.

Daraktan Janar na Hukumar Bincike da Haɓaka Kaya (RMRDC), Farfesa Nnanyelugo Ikemounso, ya bayyana cewa karkatar da fata zuwa abinci na rage muhimman kayayyakin da masana’antar fata ke dogaro da su — lamarin da zai iya kassara haɓakar da sashen ke samu a cikin shekaru masu zuwa.

Farfesan ya nuna cewa kasuwar fata ta Nijeriya ta kai kimanin dala biliyan 2.79 a 2024, kuma ana hasashen ta tashi zuwa dala biliyan 4.96 nan da 2033. Amma hakan ba zai tabbata ba idan cin ganda ya ci gaba da ruguza tanade-tanaden sashen.

“A idanun tattalin arziki da masana’antu, fatar saniya na daga cikin manyan kayayyakin da suka fi daraja a Nijeriya. Wannan ƙasa na da masana’antar fata mai ƙarfi, wadda ke iya samar da ayyukan yi, kuɗaɗen shiga daga waje, da kuma tallafa wa tattalin arzikin ƙasa,” inji shi.

“Amma ci gaba da karkatar da fata don komo na tauye wa masana’antu samun kayan aiki, yana raunana masana’antun fata da masana’antar sarrafa fata, kuma yana rage matsayin Nijeriya a kasuwar fata ta duniya.”

Farfesa Ikemounso ya jaddada cewa burin wannan yaƙi ba wai haramta komo ba ne, ko hana al’ada, sai dai mayar da fatar dabba ga amfani na masana’antu, domin ƙarfafa samar da kayayyakin fata, haɓaka fitar da su, da kuma ƙara kuɗaɗen shiga na ƙasa.

Ya ce, wannan mataki na da muhimmanci wajen kare darajar abin da gwamnati ta kira “babbbar masana’antar fata ta Nijeriya”—wato sashen fata da kayan fatarsa — wanda yanzu haka ke ba wa dubban mutane ayyukan yi daga kiwo zuwa sana’o’in hannu.

By ukarofi