Asiri ya kusa tonuwa kan wane ne ya bayar da umarnin jami’an tsaro su bar harabar makarantar GGCSS Maga

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Bisa ga dukkan alamu akwai yiyuwar asirin yadda aka yi har aka sami nasarar sace ɗaliban makarantar yan matan GGCSS Maga ranar litinin ɗin makon da ya gabata su ashirin da biyar (25).

Gwamnan jihar Kebbi Malam Nasir Idris ya nuna cewa gwamnatin sa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba har sai ta bankaɗo yadda jami’an tsaro da aka girke a makarantar suka bar harabar makarantar? Wanene ya bayar da umarnin su bar wajen a lokacin da suka bar harabar makarantar? Sannan kuma me ya sa ya bayar da umarnin? Idan kuma ba umarni aka ba su ba me ya sa suka bar harabar makarantar?
Waɗannan su ne tambayoyin da gwamnan ya kekafe ƙafa a ƙasa har sai an ba shi amsa.

Gwamnan ya yi waɗannan tambayoyin ne a lokacin da ya ke karɓar tawagar shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago da na Malamai suka kai masa ziyarar jaje dangane da sace ɗaliban.
Ya bayyana cewa mun gudanar da taron masu ruwa da tsaki kan sha’anin tsaro amma babban abin tambaya a nan shi ne, Wanene ya bayar da umarnin waɗannan jami’an tsaron su janye daga wajen kuma bayan mintuna 45 kawai aka kai harin? “Inji shi”.
Ya ce gwamnatin jihar Kebbi da ta tarayya ba za ta zauna ba har sai ta ga an ceto waɗannan ɗaliban tare da bankaɗo wanda ke da hannu wajen janye wannan jami’an tsaron da aka girke a makarantar.

Yanzu haka dai an naɗa wani kwamiti mai ƙarfi da ya ƙunshi masana harkar tsaro da su yi ƙwaƙwƙwaran bincike don gano wanda ya baiwa jami’an tsaron da aka girke a makarantar har wannan ƙazamin aiki ya faru.

Ba shakka ba za mu zauna ba za mu cigaba da ɗaukar duk wani matakin da ya dace don ganin an ceto waɗannan ɗaliban cikin salama kuma mun miƙa su ga iyayen su, sannan kuma duk wanda muka samu da hannu cikin sakaci har wannan ƙazamin aiki ya faru lallai baza mu kyale shi ba.

Ya kuma yi godiya ga ilahirin mutanen da ke tururuwa zuwa Kebbi don jajentawa bisa ga wannan lamarin tun kama daga mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima zuwa gwamnoni da hukumomi zuwa ƙungiyoyi daban-daban.

By ukarofi