Don a tabbatar da zargin kisan Kiristoci ake sace ɗalibai, inji Sheikh Gumi

Spread the love

Fitaccen malamin addinin Musulunci a Nijeriya da ke zaune a Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi, ya ce yawaitar sace-sacen ɗaliban makaranta da ake gani a ƴan kwanakin nan al’amari ne shiryayye.

A wani rubutu da ya wallafa ta kafar Facebook, Shehin malamin ya ce an dawo an shirya garkuwa da ɗaliban ne don ƙarfafa zargin waɗansu da ke son ƙaƙaba wa Nijeriya kisan Kiristoci.

Ya kuma ce halin da ake ciki yana shafar yaran addinai daban-daban, ba Kiristoci kaɗai ba.

Sannan, duk da ta’azzarar matsalar tsaro, abu ne da zai zo ƙarshe “da yardar Allah” a Nijeriya.

Sheikh Gumi na ɗaya daga cikin malaman da ke da fahimtar yin tattaunawa ta sulhu da ƴan bindiga shi ne mafita ga ayyukan sace mutane a ƙasar musamman a yankin arewacin Nijeriya.

By Babaji