
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Cocin Christ Apostlic (CAC) ta fitar da sunayen masu ibada guda 38 da aka yi garkuwa su a lokacin da ƴan bindiga suka kai farmaki a garin Eruku na Ƙaramar Hukumar Ekiti a Jihar Kwara.
Hakan na zuwa ne bayan ƙasa da kwana biyu da ƴan bindigar sukanemi a biya su kimanin Naira biliyan 3.8 a matsayin kuɗin fansarsu, wanda hakan ke nuna za a biya miliyan N100 ga kowane mutum ɗaya daga cikinsu.
Jaddawalin sunayen ya nuna cewa mai shekaru 64 daga cikin waɗanda aka sacen ita ce mafi tsufa yauinwata ƴar shekara bakwai ce ƙarama daga cikinsu.
Haka kuma guda 30 daga cikin 38 da aka yi garkuwa da su mata ne. Sannan takwas yara ne ƙanana.
Ga jerin sunayensu kamar yadda IntelRegion ta ruwaito:
“Felicia Ige (64); Timileyin Joshua (22); Elizabeth Rotimi (27); Samuel Ayodele (34); Olutokun Yetunde (23); Olutokun Janet (36); Olutokun Juwon (10), Olutokun Jumbu (12); Ebenezer Aina (24); Titilayo Balogun (59); Opeyemi Asaba (24); Grace Balogun (62), da Ayodele Taye (42).”
Sai kuma “Oloke Funmilayo (42); Joseph Olaitan (24); Eniola Princess (23); Comfort Atolani (44); Joanah Atolani (7); Imole Aina (9); Moses Ojasope (12); Iyabo Ajayi (40); Adeojo Ojasope (19); Ojo Ajayi (10); Funmilayo Joshua (64); Iyabo Michael (32); Bimpe Ige (20); Grace Iyabo Ige (41); da Deborah Peter (38).”
Kazalika, akwai “Omolola Mustapha (40); Idowu Mustapha (17); Emmanuel Bamidele (22); Ade Ajayi (7),l; Foluso Caleb (42); Funmilayo Ayodele (37); Folorunso Bamidele (42); Akinola Toluwani (24), da Akinola Babalola (14).
Al’amarin taɓarɓarewar tsaro a Nijeriya na cigaba da ta’azzara, lamarin da ke ƙara sanya fargaba acikin ƴan Nijeriya. “Gwamnatin Tarayya ta jingina hare-hare da kalaman Dona Trump na zargin kisan Kiristoci a Nijeriya.”
