
Darakta Janar na hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS) Adeola Ajayi, ya kai wa Shugaban Ƙasa Bola Tnubu rahoton halin da ake ciki game da sace-sacen ɗalibai da ƴan bindiga bindiga suka yi a jihohin Kebbi da Neja da ke arewacin ƙasar.
A sanarwar da Bayo Onanuga, Kakakin Shugaban ƙasa ya fitar, shugaban na DSS ya gana da Tinubu ne a jiya Juma’a da dare.
A ranar Litinin ne ƴan bindiga suka sace ɗalibai mata 25 daga wata makarantar sakandare ta mata a garin Maga da ke ƙaramar hukumar Danko-Wasagu a jihar Kebbi.
Sai kuma ranar Juma’a, inda aka yi awon-gaba da ɗalibai fiye da 300 da malamansu a wata sakandaren da ke Papiri a cikin Jihar Neja.
Tuni Tinnubu ya soke balaguronsa zuwa taron G20 a Afirka ta Kudu saboda halin matsalar tsaron, kuma ya tura Ministan Tsaro Abubakar Badaru Neja, yayin da Ƙaramin Ministan Tsaro Bello Matawalle ya tafi Kebbi domin shawo kan al’amuran.
