Daga JOHN D. WADA a Keffi
An gudanar da wani babban taron baje-kolin al’adu da kayayyakin gargajiya karon farko a babbar jami’ar jihar Nasarawa dake Keffi a yau Asabar 22 ga watan Nuwambar shekarar 2025 da ake ciki.
Taron wadda a ka yi wa laƙabi da ‘Arewa Festival 2025 a turance wadda Tripoint Academy ta shirya ya ƙunshi baje-kolin kayayyaki irin na al’adun garggajiya da suka haɗa da sutura da kayayyakin ƙamshi da kilishi da abinci da hawan doki da wasannin kwaikwayo da barkwanci da dai sauran su da yawa duk irin na al’adun Arewacin ƙasar nan.
Da take tattaunawa da manema labarai ciki har da wakilin mu a wajen taron, kodinetar cibiya da suka shirya taron wato Tripoint Academy, hajiya Amina Aminu ta bayyana cewa taron wadda za a gudanar da shi a kwana biyu wato yau Asabar da kuma gobe Lahadi an shirya shi ne da nufin haɗa kawunan al’ummar Arewa da isar da saƙon zaman lafiya da ƙauna tsakanin su a duk inda suke tare da baje-kolin kayayyaki da al’adun gargajiyar irin na bahaushe wa duniya baki ɗaya.
Ta ce ba shakka Allah ya albarkaci ƙasar Hausa da baiwa da kuma ni’ima da dama wanda ya zama dole a baje kolin su a duniya baki ɗaya inda ta kuma yi amfani da damar ta gode wa ƙungiyoyi da cibiyoyi daban daban daga ciki da wajen ƙasar nan da suke cigaba da haɗa kai da tallafawa don samun nasarar shirin.
Daganan sai kuma ta yi amfani da damar inda ta shawarci al’ummar ƙaramar hukumar Keffi da kewayenta dama jihar ta Nasarawa da ƙasa baki ɗaya su riƙa sayen kayayyakin gargajiya na cikin gida Najeriya musamman daga Arewa don inganta da samun bunƙasar su a idon duniya.
Tun farko a yayin bikin bude taron, kwamishinan ma’aikatar yaɗa labarai da al’adun gargajiya na gwamnatin jihar Nasarawa hon. Tanko Ibrahim wanda ya kasance babban baƙo a wajen taron ya kuma samu wakilcin daraktar ma’aikatar dake fannin gudanarwa da walwaka, hajiya Aisha Ahmed Almakura ya jaddada muhimmancin taron wadda yace ke da ɗinbin tarihi sannan ya kuma yaba wa waɗanda suka shirya tare da tabbatar musu cewa a nata ɓangaren gwamnatin jihar da ma’aikatar za ta cigaba da tallafawa da kuma mara wa duk ire-iren taron baje kolin gargajiya kamar wannan don bunƙasa harkokin al’adun a jihar da kasa baki ɗaya.
Yayi Allah wadai da halayen wasu ‘yan Arewa dake watsi da al’adun su na Hausa maimakon haka sai su rika rungumar na nasara inda yace ko kaɗan hakan bai dace ba.
Sauran manyan baƙi da suka yi jawabi ciki har da mai martaba sarkin Keffi, Alhaji Cindo Yamusa duk suma sun yaba wa hangen nesa na waɗanda suka shirya taron wato Tripoint Academy inda suka yi fatan alheri tare da kira na musamman ga al’umma baki ɗaya musamman Hausawa yan Arewa su je su ganewa idanun su ire-iren albarkatun gargajiyan da ake baje-kolin su daga yau har zuwa goben a kuma farashi mai rahusa don amfanar su da iyalan su baki ɗaya.
A ƙarshe dai wakilin mu ya kuma ruwaito cewa ya zaga filin taron inda ya ga ire-iren kayayyakin al’adun malam bahaushen da aka baje kolin su a shingaye daban daban tare da wasu abubuwan al’ajabi dake tattare da tarihin asalin bahaushe ɗan Arewa da sauran su.
