Mataimakin kwamandan Hisbah a Katsina ya ajiye aikinsa

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

A sanarwar da ya fitar mataimakin kwamanda Abba Maga Isa ya bayyana cewa ya yi murabus ne bisa radin kansa, sakamakon wasu dalilai da suka sa ba zai ci gaba da riƙe muƙamin ba.

Ya godewa mahukuntan hukumar bisa damar da suka ba shi ya jagoranci sashen Guidance and Counselling a hukumar Hisbah na tsawon lokaci.

Haka kuma ya miƙa godiyar sa ga abokan aikinsa bisa goyon bayan da suka bashi tun daga lokacin da ya hau kujerar mataimakin kwamanda har zuwa ranar da ya sauka.

Tsohon ACG ɗin ya ƙara gode wa babban kwamandan hukumar da duk ma’aikatan Hisbah baki ɗaya, yana mai addu’ar Allah ya ci gaba da kare Jihar Katsina, zaman lafiya tare da kawo ƙarshen matsalolin da ke fuskantar jihar da ƙasa baki ɗaya.

By ukarofi