AIG Atayero ya tallafa wa makarantar firamaren ‘yan sanda ta Wudil da kayan karatu

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Babban kwamandan makarantar ƴan sanda wato Police Acadamic Wudil (Polac) da ke jihar Kano ya tallafawa makarantar firamare da bencina da tebura.

Sunday Sama’ila shi ne shugaban makarantar Police Children School,
ya bayyana cewa zuwan babban hafsan rundunar ‘yan sanda, AIG Patrick Atayero, ya sauya fasalin makarantar ta fuskar ci gaba, tallafi da kuma ingantaccen shugabanci sa.

Daga cikin kayayyakin da ya samar sun haɗa kujeru guda 15 da kujeru 10 na aji, da kuma na ofis guda 10. Sai guda biyar na ofis, sai tebura guda biyar.

Ya ƙara da cewa shi ne ya sanlmar da gida na zama domin malamai ko buƙatun makaranta ya kuma amince aka samar da babban ɗakin taro, wanda yanzu ake amfani da shi wajen tarukan makaranta, musamman bikin kammala karatun yara.

Ya ce wannan taimako ya ƙara wa makarantar ƙwarin guiwa, tare da inganta jin daɗin malamai, ɗalibai da ma iyaye.

“Tun da nake a nan, AIG Atayero yana bamu cikakkiyar kulawa. Ya nuna mana cewa shi uba ne a gare mu. Muna alfahari da shi ƙwarai da gaske.”

Gudummawar AIG Patrick Atayero ga Police Children School Wudil ta ƙara tabbatar da muhimmancin shugabanci na gari, da jajircewar jami’an rundunar ‘yan sanda wajen tallafawa ilimi.

Makarantar ta ce za ta ci gaba da yin addu’a da fatan Allah ya ƙara masa basira da ikon ci gaba da ayyukan alheri.

Gudunmawar dai ta samu ne bisa ƙoƙari da jajircewa ta DCP Zakari Adamu, duka dai don bunƙasa ilimi da samun walwala a wannan makaranta.

By ukarofi