Tinubu ya yi jimamin rasuwar Sheikh Ɗahiru Bauchi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Tinubu ya bayyana kaɗuwarsa akan rasuwar babban malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi, wanda ya rasu a daren Laraba wayewar yau Alhamis.

Tinubu ya ce, samun labarin ya sanya shi cikin kaɗuwa matuƙa, yana mai bayyana jagoran na Ɗarikar Tijjaniya a matsayin mutum mai daraja da ƙima.

Haka kuma, ya bayyana shi a matsayin madubi wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen koyarwa musamman Alƙur’ani mai girma.

Shugaban ƙasar ya ƙara da cewa rasuwar shehin malamin rashi ne ga Nijeriya baki ɗaya, ba ga iyalai da ɗalibai ko mabiyansa kaɗai ba.

Kazalika, ya ce a yanzu yana tuna irin ƙarfafa gwiwar da marigayin ya ba shi a lokacin da ake shirin zaɓen 2023, lamarin ya taimaka masa wajen kaiwa ga nasara.

“Sheikh Ɗahiru Bauchi malami ne, uba ne kuma murya babba da ke amo sosai,” inji shi shugaban.

Har’ilayau, Tinubu ya bayyana shi da hadimin Ƙur’ani kuma malamin da ya sadaukar da rayuwarsa wajen koyar da zaman lafiya da tsoron Allah.

Tinubu ya yi ta’aziya ga mabiya shehin malamin a faɗin Nijeriya da ma ƙasashen waje, yana mai kira a gare su da su yi koyi da halayensa na gari domin cimma nasarori a rayuwa.

By Babaji