
Dafa BELLO A. BABAJI a Abuja
Mutane da dama ne aka yi awon-gaba da su a lokacin da wasu ƴan bindiga suka kai farmaki a yankin Isanlu Makutu zuwa Idofin da ke Ƙaramar Hukumar Yagba ta Gabas a Jihar Kogi.
A cewar ShaharaReporters, shaidu sun ce maharan sun kutsa yankin ne da tsakar rana a yau Asabar, lamarin da ya sa mutane firgita tare da gudun tsira domin neman mafaka.
Saidai har ƴan bindigar suka tafi, ba a san iya adadin mutanen da suka kwashe ba.
Majiyoyi daga yankin sun ce al’amarin ya tayar da hankalin al’umma domin hatta a ƙauyukan da ke kusa da inda aka kai farmakin mutane sun cigaba da fakewa a gida yayin da masu ababen hawa kuma suka yi ta sauya hanya.
An ruwaito cewa, an sanar da hukumomin tsaro waɗanda tuni suka baza jami’ai a yankin.
Hakan na zuwa ne kwana guda da aka ceto fasinjoji 21 ciki har da mata da jariri ɗan kwana tara bayan hare-haren ƴan bindiga a manyan titunan jihar.
