Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya sake jaddada ƙudirin gwamnatinsa na zurfafa shigar al’umma cikin tattalin arziki, ƙarfafa gudanar da mulki a matakin ƙananan hukumomi, tare da tallafa wa gidaje marasa galihu a dukkan ƙananan hukumomi 34 na jihar.
Da yake jawabi yayin ziyarar haɗe kan Jihar da aka gudanar a Ofishin ƙaramar hukumar Funtua, Gwamna Raɗɗa ya ce sabon zagayen tallafin “ya nuna jajircewarmu na ganin kowace al’umma ta amfana da muhimmin tallafi da zai inganta rayuwa da gina makoma mafi kyau.”
A cikin shirin tallafin an raba injinan nika 55, injinan ban ruwa 55, injinan ‘Robaba’ 16, babura boxer 22, injinan ɗinki 15, motocin haya 3, da kuma naira ₦20,000 ga kowane mutum cikin mutane 360 marasa galihu mazaje da mata.
Gwamna Raɗɗa ya yaba wa wannan yunƙuri, yana mai cewa irin waɗannan tallafi suna da muhimmanci wajen faɗaɗa harkokin tattalin arziki, ƙarfafa dogaro da kai, da rage talauci a matakin al’umma. Ya ce:
“Kowane abin tallafin da aka raba yau wata dama ce ga iyali su bunƙasa kasuwancin su, da gina rayuwa mai daraja. Wannan shi ne ainihin manufarmu ta ƙarfafa al’umma a matakin tushe.”
Gwamnan ya isa Funtua tare da kwamishinoni, mashawarta na musamman, da manyan jami’an gwamnati, inda suka tattauna da masu ruwa da tsaki a fannoni daban-daban irin su noma, ababen more rayuwa, ilimi, kiwon lafiya, da tsaron al’umma.
Ga waɗanda suka amfana da tallafin, Gwamna Radda ya faɗa masu cewa:
“Mun ƙuduri aniyar samar da ci gaba mai adalci a dukkan ƙananan hukumomi. Ba za mu bar kowace al’umma a baya ba a cikin hangen nesanmu na ‘Gina Makomarku’.”Inji Dikko.
Haka kuma Gwamnan ya gudanar da tattaunawar dabaru da sarakunan gargajiya, shugabannin al’umma, da mazauna yankin domin fahimtar buƙatun su da kuma inganta isar da ayyuka a yankin.
Tun da farko, shugaban ƙaramar hukumar Funtua wanda ya samar da tallafin Hon. Abdu Goya, ya gode wa Gwamna Raɗɗa kan ba wa ƙananan hukumomi cikakken ‘yancin su, wanda ya ce hakan ne ya bai wa Funtua damar aiwatar da ayyuka da tallafi da suka dace da buƙatun jama’arsu.
Ya bayyana shirin tallafin a matsayin “ɓangare na ci gaba da ayyukanmu na tallafa wa matasa, mata, ƙananan sana’o’i, da gidaje marasa galihu domin samun kwanciyar hankali da ci gaban tattalin arziki.”
Hon. Goya ya tabbatar da ƙudirin sa na ci gaba da irin waɗannan shirye-shirye da ke ƙarfafa aiki tuƙuru, inganta iyalai, da haɓaka jin dadin al’ummar Funtua.
Cikin waɗanda suka halarci taron akwai Sanata Muntari Mohammed Dandutse, tare da sauran manyan jami’an gwamnatin tarayya da ta jiha.
