
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
‘Yan bindiga a Jihar Sakkwato sun yi awon-gaba da wata amarya tare da ƙwayenta da ake gab da ɗaura aurenta yayin wani hari a Ƙauyen Chacho da ke Ƙaramar Hukumar Wurno.
Rahotanni sun bayyana cewa, al’amarin ya auku ne da misalin ƙarfe 1:30 na daren wayewar ranar Lahadi, inda suka sace ta tare da ƙwayen nata da wasu mazauna yankin guda takwas.
Baki ɗaya waɗanda aka yi garkuwar da su mata ne sai namiji ɗaya. Sannan, wani mutum ya samu rauni yayin faruwar al’amarin wanda a yanzu haka yana karɓar magani.
Mazauna yankin sun shaida wa manema labarai cewa ana shirin ɗaura auren ne a ranar Lahadin sai maharan suka farmaki al’ummar garin, lamarin da wani mazaunin ƙauyen ya bayyana a matsayin abin tausayi.
Duk da cewa bai amince a bayyana sunansa ba, ya ƙara da cewa an sanar da jami’an tsaro batun, saidai ba su samo isowa wajen ba sai bayan sa’a guda da tafiyar ƴan bindigar, jinkirin da ya fusata ƴan ƙauyen.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Sakkwato, DSP Ahmad Rufa’i ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce sun samu bayanai a kai kuma suna cigaba da aiki da su domin farauto maharan da ceto waɗanda aka sacen.
Al’amarin ya nuna yadda ayyukan garkuwa da mutane a Nijeriya musamman ta arewa ya zama ruwan dare a ƴan kwanakin nan.
Haka ma a jihar Kogi a safiyar Lahadin, inda wasu ƴan bindiga suka farmaki wata coci da yin awon-gaba da fasto da matarsa.
