‘Yan makarantar Neja da aka sace na cikin ƙoshin lafiya, za su dawo nan ba da jimawa ba, inji Ribaɗu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara akan Harkar Tsaro (NSA), Nuhu Ribadu, ya ce ɗalibai da ma’aikatan da aka sace a Makarantar St. Mary’s Private Catholic Primary and Secondary School, Papiri, dake Ƙaramar Hukumar Agwaran Jihar Neja suna cikin ƙoshin lafiya, kuma za a haɗa su da iyalansu nan kusa.

A ranar 21 ga Nuwamba ne wasu ƴan bindiga suka kai hari makarantar, inda suka yi awon-gaba da mutane 315 da suka haɗa da ɗalibai 303 da malamai 12.

Daga baya, Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen Jihar Neja ta sanar da cewa dalibai 50 daga cikin waɗanda aka sace sun tsere daga hannun ƴan bindigar.

Ribaɗu ya bayyana hakan ne a yayin ganawa da manema labarai yayin ziyara da ya kai wa CAN a Jihar Neja, inda ya ce gwamnati na aiki kafaɗa-da-kafaɗa da hukumomin tsaro domin ganin an kuɓutar da yaran cikin ƙoshin lafiya ba tare da wata matsala ba.

Ya ƙara da cewa gwamnati ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ganin an kawo ƙarshen matsalar garkuwa da mutane a Nijeriya.

A aukuwar irin wannan lamari a Jihar Katsina a shekarar 2023, inda aka sace wasu ɗalibai waɗanda daga bisani hukumomi suka samu nasarar kuɓutar da su cikin kwanciyar hankali.

By Babaji