Nijeriya ta ba ɗan takarar shugaban ƙasa na Guinea-Bissau mafaka

Spread the love

Gwamnatin Tarayya ta amince da bada kariya ga ɗan takarar shugaban ƙasar na Guinea-Bissau a ofishin jakadancin Nijeriya, wanda ya nemi mafaka a ƙasar.

Wannan mataki ya zo ne a lokacin da rikice-rikicen siyasa da rashin tabbas suka ƙara ƙamari a Guinea-Bissau tun bayan zaɓen ƙasar da karɓe mulki da rundunar sojoji ta yi.

Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin Nijeriya ta nemi goyon bayan ECOWAS domin tabbatar da cewa waɗannan matakan tsaro sun dace da ƙa’idojin yankin, tare da tabbatar da kariya da mutunta haƙƙin ɗan takarar.

Gwamnatin ta kuma ce za ta cigaba da bin duk matakan diflomasiyya domin taimakawa wajen hana rikici da inganta zaman lafiya a ƙasashen yankin Afirka ta Yamma.

By Babaji