Hanyoyin daƙile cin zarafin ƙananan yara

Spread the love

Kamar yadda kowannen mu ya sani ne yara na daga cikin ni’imomin da Allah Ubangiji yake bai wa duk wanda Ya so daga bayinSa. Haka zalika, yara amana ce da Ubangiji Ya rataya a wuyan iyaye. Don haka ne, yake daga cikin haƙƙoƙin yaran kula da cin su da shan su, da suturar su, da mahalli da kuma basu ilimi na zamani da na addini. Harwayau, da kiyaye su daga dukkan haɗari, kula da ba su ingantacciyar lafiya, na daga cikin haƙƙoƙin da ya zama wajibi iyaye su kula da su akan ‘ya’yansu.

A wannan zamani da muke ciki, abin tsoro ne da firgitarwa, yadda yara suka zama kamar dabbobin kiwo a tsakanin mugun manomi wanda zai iya kai musu hari a kowanne lokaci. Wannan ya sa rayuwar yara cikin barazana da ƙalubale. Daga cikin ƙalubale da yara suke fuskanta a wannan zamani akwai; safarar ƙananan yara, fyaɗe ko cin zarafi ta hanyar jima’i, cin zarafi na cutar wa ta jiki, watsi da rashin ba su kyakkyawar kulawa, cin zarafi ta hanyar ƙuntatawa, garkuwa da sauran ire-iren cin zarafin yara. 

Cin zarafin yara na nufin cutar da yaro ta kowacce fuska ko ta taɓa jikin yaro ko yarinya da niyyar jin daɗi ko don samun damar jima’i. Daga cikin misalan cin zarafin yara akwai taɓa jikin ƙananan yara ta hanyoyin da ba su dace ba, ko kuwa matsa wa yaro ya taɓa jikin babba ta hanyar da bata dace ba ko kuma buɗe wa ƙananan yara ido kan abubuwan da suka shafi jima’i.

A mafi yawan lokuta, ana samun waɗanda yaran suka san su kuma suke kusantar su yau da gobe, su ne suka fi cin amanarsu ta hanyar cin zarafinsu. Waɗannan mutanen wani lokaci ‘yan uwansu ne ko kuma daginsu ne. Wani lokaci ma malaman makarantun su ne, yayin da a wasu lokutan yake kasancewa abokan karatun su ne. Akwai labarai masu baƙanta rai da ake wallafawa a shafukan sada zumunta waɗanda suka ƙunshi cin zarafin yara. 

Na karanta labarin wani mutum mai shekaru 54 da ya kasance yana cin zarafin ‘ya’yansa mata har tsawon shekaru bakwai a Jihar Delta, kodayake a halin yanzu yana tsare a hannun hukuma. Abin kunya ne da takaici, ganin yadda ire-iren waɗannan labarai ke ci gaba da waruwa. Wasu akan ruwaito su a jaridu, yayin da wasu ke yaɗuwa a bakunan jama’a. 

Akwai alamomin da ya kamata iyaye su riƙa sa ido suna kulawa akai, musamman idan yaransu sun fara nuna wasu alamomin dake nuna tabbas ana cin zarafin su. Waɗannan alamomi sun haɗa da canzawar yanayin yaro lokaci guda, abin da ake nufi da turanci, sudden mood change. Sannan kuma idan an lura da yaro yana ƙauracewa wa ‘yan’uwansa ko abokansa; akwai rashin sanin takamaiman bayani akan ciwon dake jikinsa da kuma furta wasu kalmomi ko kuwa maganganu dake da alaƙa da jima’i da sauran su. Irin waɗannan abubuwa ya kamata iyaye su ɗauki ƙwararan matakai a kai.

Daga cikin hanyoyin da za mu magance cin zarafin yara sun haɗa da, na farko, sa ido akan kaiwa da komowar yara. Iyaye su tarbiyyantar da ‘ya’yansu ta hanyar tausayi, da kyautatawa da kuma bada kyakkyawar kulawa gare su. Iyaye ya kamata su lura da yanayin girman jikin ‘ya’yansu, wannan zai taimaka wajen sanin idan akwai wani baƙon canji a jikin su. Haka nan, zai taimaka musu wajen bada kulawar da ta dace akan yaran.

Hanya ta biyu, ita ce tattaunawa ta zahiri. Ya kamata iyaye su ware lokutan da za su riƙa tattaunawa da ‘ya’yansu, wanda zai taimaka wa yara su saki jiki da iyayensu wajen gaya musu duk abinda ya shafe su. Hakan nan taimakawa wajen gina alaƙa ta gaske mai cike da amana tsakanin yara da iyayensu.

Hanya ta uku, shi ne bada shawarwari kan tsaro. Iyaye su bai wa ‘ya’yansu shawarwari game da tsaro kan rayuwar su, yadda za su kare kansu daga miyagun mutane. A sanar da yara gaɓoɓin da bai kamata wani ya taɓa musu ba, a cikin hikima da dabara ta yadda za su fahimta. Haka zalika, a gaya wa yara su kai ƙarar duk wanda ya taɓa musu jikinsu ta yadda bai kamata ba, ga iyayensu ko hukumar makaranta. Sannan a koya musu dabarun fallasa duk wani mai mugun dake ƙoƙarin aikata musu wani mummunan abu, kamar lokacin da yaro zai yi ihu domin neman agaji, ko yin cizo, yayin da wani ke neman cin zarafin su ta hanyar ƙarfi.

Hanya ta huɗu ita ce, tsare yara daga tasirin shafukan sada zumunta. A yau an wayi gari kowanne irin nau’i na abubuwan da suka dace, da wanda ba su dace ba, waɗanda a kullum ake wallafa su a shafukan sada zumunta. Haka zalika, akwai miyagun mutane da suke koya wa yara fitsara da shashanci ta hanyar hirar da su a zahiri ko ta yanar gizo. Lallai ya zama wajibi iyaye su kare ‘yan’yansu daga duk abinda zai gurɓata musu tarbiyyarsu, da addininsu. Iyaye su sa ido akan waɗanda ‘yan’yansu ke hulɗa da su akan yanar gizo, musamman a shafukan fesbuk ko WhatsApp, tare da saka masu iyaka akan shafukan sada zumunta, da ilimantar da su yadda za su kare kansu daga barazanar da ake fuskanta a yanar gizo. Haka zalika, iyaye su dage wajen yi wa ‘yan’yansu addu’ar da za ta tsare su daga miyagu, da masu cin zarafin yara.

A ƙarshe, ina kira ga gwamnati ta daɗa ƙarfafa dokar hukunta masu cin zarafin yara. A tabbatar da hukunta su bisa doka domin rage yawan masu cin zarafin yara a cikin al’umma, da ɗaukar matakin tsorata wasu don ya zama darasi ga sauran al’umma. 

HASSAN IMRAN ya aiko da wannan wasiƙa ne daga Jos, kuma za a iya samunsa kan addreshinsa na yanar gizo: [email protected].

By ukarofi