Daga ALI ABUBAKAR SADIQ
Abinda na dade da ganowa ba tun yanzu ba shine, babu wata kungiyar addini da ba za ka samu cewa akwai inda ta ke daidai da kuma inda ta ke kuskure ba. Shi kuma kuskure, matukar ba ka gane shi ba to har abada ba za ka iya gyara shi ba. Don haka hanyoyin da zamu kaucewa kura-kuran mu, kuma mu zauna da juna lafiya ba su wuce wasu dokoki guda biyu da Allah ya wajabta mana cikin Qurani ba.
Ta farko ita ce mu gane cewa ba wanda zai zama cikakken musulmi mai adalci sai ya dauki koyarwar Q4:135 “Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku kasance mãsu tsayuwa da ãdalci, mãsu shaida sabõda Allah, kuma kõ dã a kanku ne kõ kuwa, mahaifa da mafi kusantar zumunta, ko (wanda ake yi wa shaida kõ a kansa) ya kasance mawadãci kõ matalauci, to, Allah ne Mafi cancanta da al’amarinsu. Sabõda haka, kada ku bĩbiyi son zũciya, har ku karkata. Kuma idan kuka karkatar da magana, kõ kuwa kuka kau da kai, to lalle ne Allah Yã kasance Masani ga abin da kuke aikatãwa.”
Wannan aya ita ce ginshikin mu’amalar musulmi kuma wallahi ita kadai ta isa ta kawo zaman lafiya a duniya, idan da za ta zama ma’aunin kowacce irin mu’amala. Saboda tasirin wannan aya, hatta wadanda ba musulmi ba sun yaba da adalcin da ke cikinta, yadda Jami’a mafi girma da ilimi a yanzu a duniya, wato Harvard University, sun kafe wannan ayar a kofar shiga sashen Shari’a na jami’ar. Ita gaskiya kwaya daya ce, amma hanyoyin isa gare ta na da yawa.
Sannan ginshikin na biyu shine bin, sau-da-kafa, umarnin Allah na yadda za’a yi wa’azi cikin Q16:125 “Ka yi kira zuwa ga hanyar Ubangijinka da hikima da wa’azi mai kyau kuma ka yi jãyayya da su da magana wadda take mafi kyau. Lalle ne Ubangijinka Shĩ ne Mafi sani ga wanda ya ɓãce daga hanyarSa, kuma Shi ne Mafi sani ga mãsu shiryuwa.”
To amma kash! gaba dayanmu muna da raunin wajen aiki da wadannan ginshikai guda biyu, shi ya sa muka bar jaki mu na bugun taiki. Kuma haka za mu dawwama matukar ba mu iya aiki da wadannan koyarwar ba.
Masussuka na da kura-kurai a game da akidar Qurani zalla da kuma gurguwar fahimta a wasu ayoyi na Qurani, sannan da kuskuren cewa Qur’ani ne kadai abin bi babu wani abu (koda yake na ga ya fara sassautowa kan hadisai). Idan muka juya cikin Qurani zamu ci karo da ayoyi da dama da ke kira zuwa ga “littafi da hikima”, duk da cewa shi kansa Qurani hikima ce, amma yadda Ayoyin su ka zo, su na raba littafi ne da wata hikima daban, domin a sauran littafai da Allah ya saukar irinsu Attaura da linjila, su ma haka ya kira su, wato “Littafi da hikima”. Kamar yadda Allah ya sanar mana cikin Q4:54 “Ko su na hãssadar mutãne ne a kan abin da Allah Ya bã su daga falalarSa? To, lalle ne, Mun bai wa gidan Ibrãhĩm Littãfi da hikima kuma Mun bã su mulki mai girma.”
Kun ga izina ce cewa ba Qurani kawai Allah ke magana ba a matsayin littafi. Domin kara tantance cewa bayan Qurani akwai wasu hanyoyi na shiriya, sai Allah ya ce Q22:8 “Kuma daga mutãne akwai mai yin musu ga Allah bã da wani;
1. ilmi ba
2. Kuma bã da wata shiriya ba,
3. Kuma bã da wani littãfi mai haskakãwa ba.”
Ka ga a tsanake Allah ya fitar mana da hanyoyi uku na shiriya a wannan aya, wato Ilimi, shiriya da littafi. Ilimi ya kunshi duk wani Ilimi mai amfani da zai amfanar da Dan Adam, kamar kimiyya, falsafa da sauransu. Ita kuma shiriya, akwai abubuwa nagari na gadon al’ada, wadanda kowacce al’umma na da irin na ta, da kuma gama-gari wanda ko ba ka addini ka yarda da su, misali kowa ya yarda da yin gaskiya abu ne mai kyau amma karya babu kyau, haka nan sata babu kyau ko a wajen barawo ne dss, sannan sai littafan da Allah ya saukar. To ta wadannan hanyoyi Dan Adam zai sami cikakkiyar shiriya wajen rayuwa tagari.
Saboda haka babu dalili da mutum zai ce yayi watsi da hadisi gaba daya, amma kuma dole, sakamakon rudani da ake samu a hadisai, a rika amfani da Qur’ani wajen tantance hadisai. Sannan Masussuka na kuskuren rushe tarihi, kamar yadda ya ke cewa babu wani Hussaini jikan Annabi, idan a irin fahimtar sa ne to da sai ace Annabi da wasu daidaikun mutane kawai su ka wanzu, amma irinsu Khadija, Aisha, Khulafa Ur Rashidun, kafiran Makka, su Kisra da Najjashi duk ba ayi su ba, tunda ba su zo a Qurani ba.
Su kuma Malaman Izala, babban kuskurensu bai wuce na rashin bin dokar wa’azi ba da Allah ya kafa a Q16:125, ta yadda wanda duk ya saba da fahimtarsu gani su ke yi tamkar ya kafirta. Sannan kusan akasarin abinda su ke zargin Yan Darika/Shi’a da shi, ya fada kansu. Misali, yadda su ke zargin yan Darika na daukar shaihunnai ko yadda Yan Shia ke daukar Ahlul Bayt, to su ma haka su ke daukar Sahabbai/Salaf/hadisi. An wayi gari cewa yadda Salafawa su ka dauki hadisi da kare shi da assasa shi ba sa yiwa Qur’ani haka. Cikinsu akwai wadanda sun yarda hadisi na iya soke Qur’ani. Sannan sun yarda cewa Sahabbai irinsu Umar za su iya soke koyarwar Qurani (misali a dauki maganar hukuncin Zina, saki uku da sauransu).
Cikin gwanintar Allah ta wahayin Qurani, ya saukar da ayoyi wadanda aikinsu ya bayyana tun zamanin Manzo, akwai kuma wasu da sai bayan wafatin sa zasu bayyana har karshen Duniya. Kuma a bayyane ya ke cewa idan ka tattara dukkan ayoyin da Annabi ya yi tafsirinsu a cikin hadisai, zaka samu ba su kai kashi daya cikin uku na Ayoyin Qurani ba. Malamai irinsu Ibn Taimiyya su na da fahimtar cewa Annabi ya yi tafsirin kowace aya, amma kuma irinsu Imam Suyuti na ja da haka.
Hujjoji na zahiri sun fi karfafa cewa ba duk Qurani Annabi yayi wa Tafsir ba, cikinsu akwai Hadisai da su ka kawo bayanin cewa ayoyin da su ka shafi Riba da kalala Annabi bai yi cikakken bayaninsu ba har ya bar Duniya. Sannan idan ka bi manyan tafsirai irinsu Ibn Kathir, Tabari, Jalalain, Tafsir Al Kabir, Tafsir Al Baghwi za ka samu babu wanda ya iya kawo hadisi bayan kowacce aya. Don haka a bayyane ya ke cewa ba dukkan Qurani Annabi ya yi tafsirinsa ba.
Wannan ya tabbatar da ayar da ke ce mana; Q20:114 “…Kuma kada ka yi gaggãwa da Alƙur’ãni a gabãnin a ƙãre wahayinsa zuwa gare ka. Kuma ka ce: “Yã Ubangiji! Ka ƙãra mini ilmi.”
Wannan aya ta nuna cewa kada Annabi ya yi gaggawar cewa sai ya yi bayanin dukkannin ayoyi Qurani (kuma tarihi da hadisai sun tabbatar bai yi tafsirin duk Ayoyin ba) saboda ba wani mahaluki da zai iya kwashe duk Ilimin da ke ciki, shi yasa Allah ya ce shi kansa ya kasance cikin addu’ar a kara masa Ilimi. Kamar yadda mu ka ga Annabi Musa a zamaninsa Allah ya tura shi wajen Khidir domin wani Ilimi da bai sani ba duk da cewa shine Annabin zamaninsa. Shi yasa Allah ya ce da Annabi kada ya yi gaggawa. To idan Annabi bai yi tafsirin duk Ayoyin Qurani ba, wanene zai yi? Sai mu duba Ayoyin Suratul ƙiyamah; Q75:16-19 “Kada ka mõtsar da harshenka game da shi dõmin ka yi gaugãwar riƙe shi (Alƙur’ãni). Lalle ne, wãjibi ne a gare Mu, Mu tãra shi. Mu (tsare maka) karãtunsa.To idan Muka karanta shi sai ka bi karatunsa. sa’an nan, lalle wãjibi ne a gare Mu, bayãninsa.”
Wannan aya ke tabbatar da cewa Allah da kansa zai rika tafsirin Qurani ga daidaikun masu fassara daga bayan wafatin Manzo har karshen Duniya. Misali a nan idan ka dauki ayar cikin Suratul Mudaththir; Q74:30 “A kanta akwai (matsara) gõma shã tara.”
Babu wani hadisi ko sahabi da ya yi tafsirin wannan aya har zuwa farkon Karni na 10, lokacin da Tabari ya yi tafsirinsa, inda daga nan ne ya fara bayanin cewa ayar na maganar adadin mala’iku ne masu tsaron wuta guda 19. Har zuwa wannan zamani namu akan haka ake tafsirin wannan aya, inda shi kuma Rashad Khalifa ya zo da lissafin 19 wanda da shi ne Allah ya daure Qurani ta yadda ba za’a iya kari ko ragi na kalma guda a ciki ba. Kamar haka Allah ya ke bayyanar da tafsirin ayoyi ga daidaikun Malamai masu fassara daidai da Ilimi da fahimtar zamaninsu.
Kuma dai mun riga mun tabbatar da cewa babu wata hujja ta zahiri da ta nuna Annabi yayi Tafsir daga Baƙara zuwa nasi, daya-bayan-dayan ayoyi. Kamar yadda na fada a baya, akwai Ayoyin da sam ba zamanin Annabi su ke magana akai ba, ayoyi ne na wasu zamunna bayan Annabi, zuwa kanmu da wadanda zasu zo nan gaba. Misalin irin wannan aya ita ce; Q57:16 “Shin, lõkaci bai yi ba ga wa ɗanda suka yi ĩmãnĩ (Musulmi) zukãtansu su yi koma ga ambaton Allah da abin da ya sauka daga gaskiya (Qur’ani)? Kada su kasance kamar waɗanda aka bai wa littãfi a gabãnin haka, sai zãmani ya yi tsawo a kansu, sabõda haka zukãtansu suka ƙẽƙashe, kuma masu yawa daga cikinsu fãsiƙai ne.”
Karara wannan aya ba da Sahabbai ko tabi’ai ta ke magana ba domin sun rayu a kan koyarwar Qurani domin babu hadisai a zamaninsu. Wannan aya na gargadi ne ga mu Yan baya, kada mu zama irin Yahudu da Nasara, wato bayan tsawon zamani da ya shude a kanmu, mun mayar da Qur’ani kurar baya, ya na biye da hadisai da Fiƙihu wadanda su ka saba da wasu koyarwarsa. Shin lokaci bai yi ba da zamu daina yiwa Qurani karatun Aku, mu komo aiki da koyarwarsa ba? Shine gargadin da wannan aya ke mana. Idan kuwa mu ka ki, to mu sani cewa, daya daga cikin irin Ayoyin da aikinta sai nan gaba ita ce wadda a ranar Lahira, Annabi da kansa zai kai karar mu wajen Allah cewa; Q25:30 “Kuma Manzo ya ce: “Ya Ubangijĩna! Lalle mutãnena sun riƙi wannan Alƙur’ãni abin ƙauracẽwa!.”
Wato duk da Annabi ya bar mana cikakke, kuma kammalallen Qurani, sai mu ka kaurace masa ta hanyar saka hadisai da Fiƙihu gaba, wato yadda Qurani zai fadi hukunci amma a yi watsi da shi a dauki hadisi ko Fiqihu a yi amfani da shi. Wato a aikace mun dabbaka cewa hadisi ko Fiƙihu na iya shafe hukuncin Qur’ani kenan. Kaga mun nuna ba ruwanmu da aikata Quranin a aikace, mun kaurace masa a zahiri kenan, abinda Annabi zai yi wa Allah korafi a kan mu ranar Lahira.
A fahimta ta kuskuren yan Qurani zalla bai wuce na kore Hadisi gaba daya ba, su kuma Yan Izala fifita hadisi kan Qur’ani.
A ƙarshe, fatanmu shine Allah ya bamu ikon gyara kura-kuran mu gaba daya. Mu rabu da rabe-raben kungiyanci mu dawo kan abubuwa da su ka hade mu a matsayin al’umma Musulma irin wadda Allah ya yi alfahari da magabatan mu da ita a wannan siffa; Q3:110 “(Musulmi) Kun kasance mafi alhẽrin al’umma wadda aka fitar ga mutãne, ku na umurni da alhẽri kuma ku nã hani daga abin da ake ƙi, kuma ku nã ĩmãni da Allah.”
Jummu’a Mubarak!!!
