Kungiyar ɗakunan karatu ta buƙaci gwamnati ta ƙarfafa ta

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

An yi kira ga gwamnati ta bayar da kulawa wurin gudnar da ayyuka da dokar ƙasa ta tanada na kyautata ɗakunan karatu saboda gudanar da ɗakunan karatu a Nijeriya haƙƙi ne da ya dogara ga Gwamnatin Tarayya da na jihohi da na ƙananan hukumomi.

Dakta Lawan Umar Shugaban ƙungiyar masu kula da ɗakunan karatu na ƙasa ne ya yi kiran a yayin taron shekara da ƙungiyar reshen jihar Kano suka gudanar a jami’ar Khalifa Isyaku Rabiu a ranar Talata.

Ya ce, idan za a inganta ɗakunan karatu su mayar da wurin mai kyakkyawan yanayi da kowa zai yi sha’awar ya je, asa kayan aiki a ɗauki ma’aikata da suka dace, za su taimaki ɗakunan karatun saboda yanzu yanayi da suke ciki in kaje ba zaka yarda ɗan ka ya shiga ba.

Ya ce waje ne da kamar ba a ɗauke shi da muhimmanci ba, shi yasa duk abinda muke gani a ƙasar nan yake faruwa saboda al’umma bata karatu, bata tunani bata yin nazari domin al’ummar da take karatu ita take nazari da tunani 

Dakta Lawan Umar ya ƙara da jaddada cewa su kiransu ga Gwamnati ta duba makomar ƙasarnan tun daga ’ya’yanmu har zuwa shugabanni ya dogara ne ga yin karatu kuma wajibi ne a dubi karatu da ake a cikin littatafai a ɗakunan karatu tun daga makarantun firamare da Sakandire da jami’o’i da kuma ɗakin karatu na al’umma.

Shugaban ƙungiyar masu kula da ɗakunan karatun na ƙasa ya ce dama taron na matakin jihohi ana shirya shine shekara shekara bisa umurni da uwar ƙungiyar ta ƙasa ke baiwa jahohi su je su yi taron bayan anyi na ƙasa shi yasa yazo wannan taro na jihar Kano.

Ya yaba da yanda taron ya yi armashi da yanda ya gudana ya kuma jinjinawa shugabannin ƙungiyar na jihar Kano ƙarƙashin Malam Nazir Muhammad bisa himma da suka nuna wajen farfaɗo da ƙungiyar na masu kula da ɗakin karatu na jihar Kano dama ƙungiyar ta sa kai ce, bai zama wajibi don kana mai kula da ɗakin karatu ka shiga ba.

Ya ƙara da cewa, babu wata doka da ta tilasta sai ka shiga ƙungiyar, amma akwai hanyoyi da suke bi suna jawo hankalin mambobinsu tun daga kan shugabanni zuwa na ƙasa su shiga , saboda sun lura wasu shugabannin basa baiwa abin muhimmanci shi yasa suma na ƙasa dasu basa ɗaukar abin da muhimmanci.

Dakta Lawan Umar ya yi nuni da cewa amma bisa ƙoƙarinda ƙungiyar take a Kano da kuma matakinda suke ɗauka a ƙasa abubuwa na canzawa kuma za a riƙa ganin cigaba suna jawo hankalin mambobin nasu daga shugabanni zuwa na ƙasa dasu,

Shima shugaban ƙungiyar na masu kula da ɗakunan karatu reshen jihar Kano wanda kuma shine babban mai kula da ɗakin karatu na jami’ar Khalifa Isyaka Rabiu.Malam Nazir Muhammad ya ce taro ne don farfaɗo da ɗakunan karatu ta hanyar ƙirƙire ƙirƙire da zasu taimakawa maziyarta ɗakunan karatun, musamman ɗalibai ta hanyar amfani da fasaha.

Ya ce, taron shine karo na biyu a jihar Kano amma a ƙasa anyi karo na 63.Kuma taron na bana a Kano ya haɗa mambobin ƙungiyar har na wasu jihohin ƙasarnan sun halarta.

Ya ce, a matsayinsa na ɗaya daga nambobin Shugabanin ƙungiyar har Allah ya kawo su lokaci da ya zama shine shugabanta na jihar Kano ya san matsalolin ƙungiyar da yawa, da yazo sai ya soma duba muhimman abubuwa da yakamata zata yi na farko .

Don haka dole ta ga.yakamata ta riƙa shirya irin wannan taruka na ƙarawa juna sani dan horar da yan ƙungiyar sanin makaman aiki kamar yanda suke yi yanzu ,haka kuma sun yi tarurruka na bita da yawa akan yanda za a sami damar yin amfani da fasaha wurin kyautata cigaban ɗakunan karatu.

Sannan ya ga yakamata ace ƙungiyar ta dawo da mujalla idan mambobinta sun je sunyi bincike sun gabatar da ƙasidu za su zo su buga a ciki, saboda ba zaka sami ƙarin girma ba sai ka kawo irin waɗannan ƙasidu yanzu an dawo anayin mujallar da kafar sadarwa.

Ya ce daga cikin ƙalubale da suke fuskanta shine suna da mambobi da yawa a Kano amma mafi yawa a wannan taron da suka zo daga wajen Kano suke akwai buƙatar ƙungiya ta ƙara haɗa kai shi yasa da suka zo suka riƙa zagayawa duk inda suka san akwai ɗakin karatu ake nuna musu muhimmancin bunƙasa martabar ƙungiyar.

Malam Nazir Muhammad ya yi kira ga gwamnati ta taimaka musu domin duk ɗawainiya da ake da kuɗi ake, musamman na shirya irin wannan taron suna buƙatar Gwamnati ta riƙa shigowa al’amuran su tana taimakawa saboda mafi yawan mambobinsu yan jihar Kano ne, kuma mafi yawa a makarantun jihar Kano suke aiki mafi yawa ɗalibai da suke taimakawa a ɗakunan karatun yan jihar Kano ne.

Hajiya Mabaruka Abubakar Abba Babbar mai kula da ɗakin karatu na kwalejin ilimi ta Sa’adatu Rimi wacce ta taɓa zama ma’aji a ƙungiyar masu kula da ɗakunan karatu na jihar Kano ta bayyana cewa taron dama duk shekara ana yinsa, bana ma sunyi taron ne akan harkar cigaban ɗakunan karatu, kuma ta yaba da yanda aka gudanar da taron.

Ta ce, taron ya sami halartar ‘yan ƙungiyar kuma babban sakataren kula da ɗakin karatu na jihar Kano ya zo taron kuma ya ce Gwamnati tana ɗaukar nauyin gyara ɗakunan karatu akwai guda takwas an soma gyarawa a ƙananan hukumomi an gyara wasu an sa musu kayan sadarwa na zamani ba sai sun zo babban ɗakin karatu na jiha ba. ɗakin karatu na jama’a na anyi masa gyara sosai.

Suna fata Gwamnati ta cika musu burinsu a matsayin su na masu kula da ɗakunan karatu a gyara ɗakunan karatu na ƙananan hukumomi 44 ya zama yara a duk inda suke zasu iya amfani da ɗakin karatu ba sai sun zo jiha.

Hajiya Mabaruka Abubakar Abba ta ce a matsayinta ta nace mai kula da ɗakin karatu tana sha’awar aikin kuma tana kira ga yan’uwanta mambobin ƙungiyar su haɗa kai suyi abinda yakamata kamar biyan kuɗi na ƙungiya da kula da harkokin ci gabanta.

By ukarofi