Kungiyar masana zane-zane ta koka kan gobarar da ta laƙume Herwa Heart of Art Gallery

Spread the love

Daga WAKILINMU

Sanannen wajen koyar da fasaha na Herwa Heart of Art Gallery, wacce ta shahara a matsayin babban cibiyar ƙirƙira kuma ta samu lambar yabo ta Outstanding Gallery Award daga ƙungiyar ɗaliban Zane-Zane ta Nijeriya (SNA), ta ƙone ƙurmus a ranar Juma’ar da ta gabata sakamakon abin da shaidun gani da ido suka bayyana a matsayin fashewar hasken rana kwatsam.

Wannan lamari ya tayar da hankulan maƙota da ke yankin.

Akan haka ne ƙungiyar SNA ta bayyana al’amarin a matsayin babban rashi ba ga ‘yan ƙungiyar ba kaɗai har ma ga ɗalibai masu tasowa, asarar a matsayin babbar rashi ga masu zane-zane, masu sha’awar fasaha da kuma al’ummar da ta daɗe tana ganin wannan gallery a matsayin cibiyar ƙirƙira da adana al’adunmu na Arewa.

A sanarwar da ta fitar a ranar Litinin ta hannun Sakatariyar yaɗa labaranta, Binta Abba, ƙungiyar ta mika saƙon jajenta ga shugabar gallery Herwa Heart kuma babbar jamia a ƙungiyar, Hajiya Kaltume Bulama Gana (fsna).

Ta kuma yaba mata bisa hangen nesa, jajircewa wajen inganta fasaha, da muhimmiyar gudummuwar da ta ke bayar wajen cigaban fasahar a Nijeriya.

An yaba mata ƙwarai da gaske wajen jajircewarta dan zaburar da al’ummomi tsawon shekaru, inji sanarwar wanda wannan babban abundubawa ne ba nata kaɗai ba ne, rashi ne ga dukkan masu fasahar a Nijeriya.”

ƙungiyar ta Nigerian Society of Artist SNA ta kuma tabbatar da cikakkiyar goyon bayanta ga Hajiya Gana a wannan mawuyacin lokaci, tare da tabbatar mata da shirinta na mara mata baya har tsawon lokacin farfadowa da Herwa Heart of Art Gallery. Haka kuma kungiyar ta yi alƙawarin yin aiki tare da ita da sauran masu ruwa da tsaki domin gina sabo, farfaɗo da ayyuka, da ci gaba da tabbatar da gadon kirkira da ƙirƙire-ƙirƙire da Herwa Heart of Art Gallery ke wakilta.

By ukarofi