Manoman shinkafa sun hango ƙarin faɗuwar farashi a Legas

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kungiyoyin manoman shinkafa a Jihar Legas sun yi hasashen cewa farashin shinkafa zai ƙara sauƙa a kasuwa gabanin bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara, bayan matakin da Gwamnatin jihar ta ɗauka na rage farashin shinkafar Legas daga N64,000 zuwa N57,000 a kan kowanne buhu.

Manoman sun bayyana haka ne a hirarraki daban-daban da suka yi da wakilan Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya a ranar Lahadi a Legas.

Rahoton ya nuna cewa gwamnatin Jihar Legas, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Babajide Sanwo-Olu, ta yanke wannan mataki ne domin rage raɗaɗin tsadar rayuwa da kuma tallafa wa al’umma a daidai lokacin bukukuwa.

Mataimakin Shugaban ƙungiyar Manoma ta Yankin Kudu-maso-Yamma da reshen Jihar Legas, Sakin Agbayewa, ya yaba wa gwamnatin jihar bisa wannan tsari da ya ce an dauke shi bisa hangen nesa da la’akari da halin da al’umma ke ciki.

A cewarsa, ɗaura farashin buhun shinkafa a N57,000 zai haifar da gasa tsakanin masu sayarwa da masu shigo da shinkafa, wanda hakan zai tilasta ƙarin saukar farashi a kasuwa.

“Matakin Gwamnatin Jihar Legas na daura farashin buhun shinkafa a N57,000 babbar alheri ce. Muna kyautata zaton cewa da wannan gasa da aka bude, a cikin mako guda ko biyu masu zuwa, farashin zai iya ƙara sauka,” inji Agbayewa.

Ya kara da cewa a halin yanzu farashin shinkafar waje yana tsakanin N52,000 zuwa N56,000, gwargwadon inda ake saye.

A cewarsa, idan ana saye a kusa da iyaka, ana iya samu a N52,000, amma idan a manyan kasuwanni ne, yana kaiwa N54,000 zuwa N55,000 sakamakon ɗora kuɗin sufuri.

Agbayewa ya ce bambancin da ke tsakanin shinkafar Legas da ta waje ba wai farashi ne kawai ba, har da inganci da tsaron abinci. “Idan ka sayi shinkafar Legas a N57,000, kana cin abinci mai inganci. Daga noma zuwa nika, sarrafawa, adanawa zuwa kasuwa da mabuƙaci, yawanci wannan shinkafa tana ɗaukar kimanin shekara guda ne. Amma shinkafar waje da ake sayarwa a tsakanin N52,000 zuwa N56,000, akwai yiwuwar ta jima a ajiye na tsawon shekaru uku zuwa biyar, ko ma ta kusa kare wa’adin amfani,” inji shi.

Ya jaddada cewa idan aka haɗa farashi da inganci, shinkafar Legas ta fi dacewa da mabukaci, domin tana bada tabbacin tsaron abinci da ƙimarsa ta gina jiki.

“Ni kaina zan fi son in sayi shinkafar Legas a N57,000, fiye da in sayi shinkafa mai araha amma mara inganci. Idan ka sayi shinkafar Legas, kana sayen lafiya da inganci tare da darajar abinci,” inji Agbayewa.

Shi ma Shugaban ƙungiyar Manoman Shinkafa ta Nijeriya reshen Jihar Legas, Raphael Hunsa, ya yi ƙarin haske tare da yaba wa gwamnatin jihar bisa abin da ya kira mataki na jin-ƙai da kishin al’umma. A cewarsa, gwamnati ta nuna cewa tana tsayawa tsayin daka wajen daukar matakan da suka shafi jin daɗin jama’a, musamman a lokacin da tsadar rayuwa ke matuƙar damun talakawa.

“Gwamna Sanwo-Olu ya ɗauki gagarumin mataki ta hanyar rage farashin shinkafa, wannan abu ne da ya dace da a yaba. Idan samarwa ta yi ƙasa, to buƙata za ta yi yawa kuma hakan zai kai ga tashin farashi. Amma ganin cewa gwamnati ta shigo tsakani ta ɗaura farashi a N57,000 a wannan lokaci, hakan alheri ne ga ‘yan Nijeriya,” inji Hunsa.

Ya buƙaci gwamnatin jihar da ta ci gaba da tallafa wa manoma domin a samu ƙarin samarwa a duk tsawon shekara. A cewarsa, idan noman shinkafa ya riƙa gudana ba tare da tsayawa ba, to farashi zai daidaita kuma kayayyakin abinci za su ƙara sauƙa. “Idan muka samu manoma masu noma a tsawon shekara, farashin shinkafa zai daidaita, kuma ba za mu dinga fuskantar tashin farashi ba duk sanda bukukuwa suka zo,” ya ce.

Hunsa ya kuma bayyana cewa sauƙar farashin shinkafa a wannan lokaci zai taimaka matuƙa wajen sauƙaƙa wa al’umma shirye-shiryen bukukuwan Kirsimeti. “Yanzu bukukuwan Kirsimeti sun zo ƙofa, kuma kowa na son ya yi shagali. Wannan mataki zai bai wa jama’a damar yin bukukuwansu cikin walwala ba tare da matsanancin nauyi ba,” inji shi.

Masana harkokin noma sun bayyana cewa matakin Gwamnatin Legas na iya zama abin koyi ga sauran jihohi, musamman a lokacin da ake bukatar tsare-tsaren da za su rage tsadar rayuwa. Wasu daga cikinsu sun ce idan har aka samu cikakken tallafi ga manoma, kamar rangwamen kuɗin taki, iri, injinan noma da sauƙaƙe hanyoyin sufuri, to farashin ba kawai shinkafa ba, har da sauran hatsi da kayan abinci zai ƙara sauƙa a faɗin ƙasa.

A gefe guda kuma, wasu ‘yan kasuwa suna ganin cewa ɗaura farashi ta gwamnati na iya fuskantar ƙalubale idan ba a yi cikakken sa ido ba, saboda yiwuwar dillalai su boye kaya domin su sake tsada a kasuwar bayan an wuce lokacin bukukuwa. Sai dai gwamnati ta sha alwashin cewa za ta ci gaba da sanya ido da tabbatar da cewa shinkafar da aka daura farashinta a N57,000 na isa hannun mabukata ba tare da cikas ba.

A ra’ayin jama’a, sauƙar farashin shinkafar Legas ta zo a lokacin da talaka ya fi buƙatar sauƙi. Da dama sun bayyana cewa shinkafa ta zamo muhimmin bangare na abincin yau da kullum a gidajen Nijeriya, kuma duk wani canji a farashinta na shafar lafiyar tattalin arzikin iyali kai tsaye. Saboda haka, hasashen manoma na ƙarin sauƙar farashi ya haifar da sabon fata ga jama’a gabanin bukukuwan karshen shekara.

Masu saye a kasuwanni da dama a Legas sun tabbatar da cewa sun fara ganin sauƙin farashi a wasu wurare tun bayan sanarwar da gwamnati ta yi. Wasu sun ce ko da shinkafar waje ce, farashinta ya fara lankwasa ƙasa, alamar cewa kasuwa ta shiga yanayin gasa. Wannan na nuna cewa matakin gwamnati bai tsaya ga shinkafar Legas kaɗai ba, har ma yana shafar tsarin farashi a kasuwar baki ɗaya.

A ƙarshe, manoman shinkafa sun buƙaci a tabbatar da ɗorewar wannan tsari, ta hanyar ci gaba da tallafi, sa ido da inganta kayayyakin more rayuwa da ke da alaƙa da noma. Sun yi imanin cewa idan aka hada waɗannan matakai gaba daya, za a samu ba sauƙin farashi kawai ba, har ma ingantacciyar wadatar abinci ga ‘yan Nijeriya.

By ukarofi