
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rundunar ƴan sanda a Jihar Benuwai, ta kama wani da ake zargi da hannu a manyan hare-haren da suka yi sanadin rasa rayukan jami’ai a jihohin Benuwai da Nasarawa.
A cewar ƙwararre akan lamuran tsaro, Zagazola Makama, an kama wanda ake zargin ne ai suna Yongu Justine Makwagh daga Kadarko, Nasarawa da misalin ƙarfe 8 na daren Juma’a, a garejin Balcony Park da ke Makurɗi bayan tsawon watanni ana neman sa ruwa-a-jallo.
Ya ce, an gudanar da atisayen kamen ne bayan samun wasu bayanan sirri ƙarƙashin DPOn yankin Daudu da haɗin-gwiwar jami’an leƙen asiri da ke aiki na musamman.
A cewar wata majiya, an daɗe da sanya Makwagh a sahun waɗanda ake nema bisa hannu a munanan hare-hare a yankin Sankera.
Hukumomin ƴan sanda sun bayyana kamen a matsayin wata babbar nasara a ƙoƙarinsu na daƙile ayyukan ta’addanci a Benuwai da jihohin da ke maƙotaka da ita.
Haka kuma sun tabbatar da cewa a yanzu haka mai laifin yana hannu inda ake cigaba da gudanar da bincike akansa. Daga ciki akwai ƙoƙarin gano ƙarin wasu makamai da farauto waɗanda suke aiki tare da shi.
A ƴan makonni kaɗan da suka gabata ƴan bindiga sun yawaita kai farmaki musamman a makarantu da wuraren bauta, lamarin da ya jefa al’umma da dama cikin firgici, wanda kuma hakan ya sa Shugaba Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a ɓangaren tsaro domin magance matsalar.
