Rundunar sojoji ta dakatar da karɓar ritaya daga jami’anta

Spread the love

Rundunar Sojin Nijeriya ta dakatar da dukkan nau’ukan ritaya ga wasu zaɓaɓɓun hafsoshi bayan Shugaba Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-baci akan lamuran tsaron ƙasa.

A wata takarda da rundunar ta fitar a ranar 3 ga watan Disamba, ta ce an ɗauki matakin ne domin a cigaba da amfani da ƙwararrun hafsoshi yayin da ake faɗaɗa yawan dakarun saboda rashin tsaron da ya ta’azzara.

Dakatarwar ta shafi waɗanda suka kure a shekarun aiki.

Rahotanni sun ce hafsoshin da ba sa son ƙarin wa’adin za su iya yin ritaya kamar yadda aka saba, amma wadanda suka cigaba da aiki ba za su sake samun ƙarin girma ko wasu manyan damar cigaban aiki ba.

Haka kuma, rundunar ta ce matakin na ɗan lokaci ne kuma za a sake duba shi idan tsaro ya inganta a ƙasar.

By Babaji