
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara akan Harkar Tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribaɗu ya ce ya gana da tawagar ƴan majalisar Amurka a yau Lahadi a Abuja.
Hakan na zuwa ne bayan da ta iso Nijeriya domin bincika gaskiyar iƙirarin yi wa Kiristoci kisan gilla da ya tada hazo a makonnin da suka gabata.
Ribaɗu ya bayyana cewa ya gana da wakilan kuma zuwan tawagar na cikin abubuwan da suka amince da shi a tasu ziyarar da suka kai birnin Washington a watan Nuwamba.
A wani saƙo ta kafar X Ribaɗu ya ce tawagar ta ƙunshi ƴan majalisar wakilai kamar su “Mario Díaz-Balart, Norma Torres, Scott Franklin, Juan Ciscomani, da Riley M. Moore.”
Haka ma Jakadan Amurka a Nijeriya, Richard Mills, wanda yana ɗaya daga cikin ƴan tawagar.
NSAn ya ce sun tattauna matakan yaƙi da ta’addanaci da zaman lafiya a Afirka, da hanyoyin ƙarfafa ƙawancen tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka.
Gwamnatin Tarayya dai ta sha musanta ikirarin ana yi wa Kiristoci ko wata ƙabila kisan kiyashi a ƙasar, tana mai jaddada yadda al’amarin ke shafar kowane ɓangare.
