
Shugaban ƙasar Faransa, Emmanuel Macron ya ce ƙasarsa za ta taimaka wa Nijeriya shawo kan matsalar tsaro a arewacin ƙasar da ke fuskantar taɓarɓarewa.
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na dandalin X, Macron ya ce ya nemi sauran ƙasashe ƙawayensu da su “ƙara ƙaimi a hulɗarsu” da Nijeriya.
“Na yi magana da Shugaban Najeriya Bola Tinubu, na shaida masa goyon bayan Faransa game da matsalolin tsaro musamman a arewacin Najeriya,” a cewar Macron.
“Kamar yadda ya [Tinubu] buƙata, za mu ƙarfafa hulɗarmu da hukumomi da kuma taimaka wa al’ummomin da lamarin ya shafa. Bai kamata mu zama ‘yan kallo ba.”
Kalaman Macron na zuwa ne yayin da Shugaban Amurka Donald Trump ke zargin gwamnatin Nijeriya da ƙyale ‘yanbindiga suna yi wa mabiya addinin Kirista kisan gilla, iƙirarin da gwamnatin Tinubu ta musanta.
