
Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara, ya bayyana Shirin Ci-gaban jihar a matsayin dogon tsari na shekaru goma da aka gina bisa shaidu da bincike, wanda ke bayyana burin jama’a da muradun haɗin kai wajen sauya jihar zuwa mataki na ci-gaba.
Gwamnan ya ƙaddamar da shirin ne a ɗakin Sakatariyar JB Yakubu da ke Gusau a ranar Juma’a.
Wata sanarwa daga Kakakin gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ta bayyana cewa gwamnatin jihar ta ɗauki kamfanin KPMG Advisory a matsayin babban mai kula da tsara shirin.
Sanarwar ta kuma da ce KPMG yayi aiki kafaɗa da kafaɗa da mambobin Majalisar Zartarwa ta Jihar Zamfara da dukkan masu ruwa da tsaki, ciki har da shugabannin gargajiya da addini, na tsawon watanni takwas wajen kammala shirin cigaban shekaru goma.
A yayin ƙaddamarwar, Gwamna Lawal ya jaddada cewa wannan shi ne shiri na farko na dogon lokaci da aka tsara dalla-dalla a tarihin jihar a ‘yan shekarun nan.
Ya ce, “An gina shirin cigaban ne bisa bayanai ingantattu, tattaunawar masu ruwa da tsaki, da kuma daidaitawa da tsare-tsaren cigaban ƙasa da na duniya, ciki har da Manufofin Cigaba Mai Dorewa (SDGs), Tsarin Cigaban Najeriya 2050, da Tsarin Kungiyar Tarayyar Afrika na 2063.
“Shirin ya bada fifiko ga fannoni daban-daban, sakamako masu auna aiki, tare da tsarin sa ido da tantancewa wanda ke tabbatar da gaskiya da bayyana bayanai a kowane mataki na aiwatarwa.
“A cikin wannan Shirin Cigaban Jihar, mun hango Zamfara a matsayin misali na cigaban tattalin arziki mai sauya al’umma — ba kawai ga Najeriya ba, har ma ga nahiyar Afrika.
“Za mu yi amfani da albarkatunmu, kirkire-kirkire, da kyakkyawan tsarin mulki wajen inganta cigaba mai hade da kowa, zaman lafiya, da damar ci gaba. Shirin ya ta’allaka ne kan ginshikai guda shida: Tattalin Arziki; Ayyukan More Rayuwa; Jin Dadin Jama’a; Habaka Kwarewar Dan Adam; Kyakkyawan Mulki; da Cigaban Muhalli Mai Dorewa.
“Karfin Zamfara a fannin noma da albarkatun kasa zai karu ta hanyar hadin-gwiwa kamar yarjejeniyar MoFI da tallafin Bankin Cigaban Afrika. Wannan zai karfafa noma na zamani, sarrafa kayayyakin gona, da bunkasa sarkar samarwa, samar da ayyukan yi, kara wadatar abinci, buɗe kasuwanni, da rage talauci da rashin tsaro.”
Gwamna Lawal ya bayyana cewa Zamfara na kan madaidaiciyar turba. “Da Shirin Cigaban Jihar, ba wai muna mafarki ba ne — muna shirye-shiryen cimmawa. Muna sake rubuta makomar jiharmu. Muna dawo da fatan matasa, mutunci ga mabuƙata, dama ga masu kokari, da zaman lafiya ga kowa.
“Bari ƙaddamar da Shirin Ci-gaban Jihar Zamfara 2025–2034 ya zama ba wata manufa ta siyasa kawai ba, sai dai wani sabon shafi a tarihin jiharmu. A ce lokacin da Zamfara ta fuskanci mawuyacin hali, mun tashi ba da surutu ba, amma da tsayayyen kuduri. Ba da alkawurran banza ba, amma da tsare-tsaren da suka dace. Ba da bakin ciki ba, amma da hangen nesa.
“Mata da maza masu girma, jama’ata na Jihar Zamfara, da cikakken tawakkali ga Ubangiji Allah, da bangaskiya ga jajircewar al’ummarmu, da kuma cikakken kuduri ga ka’idojin da muka gabatar yau, da sunan Allah Mai Rahma, ni ne nake da girmamawa da alhakin kaddamar da Shirin Cigaban Jihar Zamfara 2025–2034 — domin yau da gobe.”
Tun da farko, jawabai sun gabata daga Sakataren Gwamnatin Jihar, Mallam Abubakar Nakwada; Shugaban Ma’aikata, Mukhtar Lugga; da Kwamishinan Kasafi da Tsare-tsare, Abdulmalik Abubakar Gajam.
