Satar ɗalibai: Mu taimaka a samar da tsaro a makarantun ’ya’yan mu

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Yayin da nake wannan rubutu, har yanzu ɗalibai kimanin fiye da 300 na makarantar firamare da sakandire ta St. Mary’s Catholic dake Papiri a Jihar Neja da suka haɗa maza da mata, suna can hannun ‘yan ta’adda masu ɗauke da makamai a cikin daji, tun bayan da aka sace su kuma aka yi garkuwa da su a makarantar da suke neman ilimi a ranar 12 ga watan Nuwamba. Wannan ya biyo bayan garkuwa da ɗaliban makarantar ‘yan mata ta Maga su 25 da wasu ‘yan ta’adda suka yi, waɗanda daga baya suka samu ‘yancin kansu, yayin da a cikin wannan makon mai ƙarewa Babban Mai Bai Wa Shugaban ƙasa Shawara Kan Sha’anin Tsaro, Nuhu Ribadu ya bayyana cewa, ana shirye-shiryen kuɓutar da su kowanne lokaci daga yanzu.

Wannan abu ne mai matuƙar ɗaga hankali ba kawai ga su yaran da aka jefa su cikin ƙunci da tagayyara ba, har ma da iyaye da malamansu, waɗanda ke cikin zullumi na rashin sanin halin da yaran su ke ciki. Wasu rahotanni ma sun bayyana cewa, akwai wani mahaifi da ya rasa ransa sakamakon ɗauke masa yaransa uku da aka yi a cikin ɗaliban makarantar firamare da sakandire ta Papiri da ke Jihar Neja.

Tun daga shekara ta 2014 da mayaƙan ƙungiyar Boko Haram suka sace ɗaliban makarantar ’yan mata ta Chibok su fiye da , kawo yanzu an sace zalibai 1,880 a sassa daban-daban na ƙasar nan, akasarin su mata ne. Kuma tun lokacin har kawo yanzu gwamnati ta kasa ɗaukar tsauraran matakai na hana cigaba da aukuwar hakan. Yayin da aka bar akasarin makarantun mu a cikin wani yanayi na takaici da sakaci. Wasu makarantun a kusa da dazuka suke a bayan gari babu kyakkyawan tsaro, wasu a bakin hanya babu kewayayyiyar katanga, ga dakunan kwanan ɗalibai babu wata kariya da za ta tsare su daga sharrin mahara. Hatta inda suke da tsarin da za a iya cewa sambarka, tsaron da suke sanya sanyawa ba wani tsaro ne mai kyau ba, wanda idan ‘yan ta’adda sun zo za su iya tunkarar su. Wasu masu gadin da ake ajiyewa ba su da wani horo na musamman, ba su da makami mai kyau, ballantana su tsorata masu mugun nufi.

Wannan na daga cikin dalilan da suka jawo iyaye da dama tsorata da gaggawar kwashe yaransu da ke makarantun kwana, bayan samun labarin harin da aka kai makarantar St Mary’s Catholic School da ke Papiri a Jihar Neja, ƙasa da mako guda bayan harin da aka kai makarantar sakandiren ’yan mata ta GGSS Maga a Jihar Kebbi. Kafin gwamnatocin jihohi da Ma’aikatun Ilimi su sanar da rufe makarantu a jihohin su, musamman jihohin da suke fuskantar ƙalubalen tsaro, irin su Sakkwato, Zamfara, Katsina, Neja, Bauchi, Taraba da Filato. A daidai lokacin da akasarin makarantun ke shirye-shiryen fara jarabawa.

Wata tambaya da ta taso shi ne, yaya gwamnati za ta samar da tsaro a makarantun yaranmu? Muna sane da cewa, gwamnati ba ta da wadatattun jami’an tsaro da za su yaƙi ‘yan ta’adda a wuraren da suka yi sansani. Don haka ne ma aka janye jami’an tsaron da ke samar da kariya ga manyan jami’an gwamnati da ‘yan siyasa, tare da shirin ɗauke jami’an soji da ke aiki a shingayen hanyoyin ƙasar nan, domin samun ƙarin jami’an da za su taimakawa waɗanda ke fafatawa a cikin daji. Kuma ba za mu cigaba sa ido yaran mu na zaune a gida babu karatu ba, don babu wanda ya san lokacin da za a kawo ƙarshen wannan barazana ta tsaro.

Sannan, a ina aka kwana kan batun sabon shirin da gwamnati ta ɓullo da shi na samar da tsaro a makarantu, wato Safe Schools Initiatiɓe, wanda aka ƙaddamar da shi a wasu jihohi da ke fuskantar matsalolin tsaro? Bincike ya nuna cewa, daga cikin manufofin kafa hukumar, akwai samar da ingantaccen tsaro a makarantu, samar da rahoton gaggawa a yayin da aka samu alamun da ke nuna barazanar tsaro ko shirin aukuwar wani mummunan al’amari. Akwai kuma sake inganta tsarin wasu makarantun da ke fama da matsalar lalacewa da sauransu. A irin wannan lokaci da harkar ilimi da gudanarwar makarantu ke fuskantar ƙalubalen tsaro, babu wani abu da wannan shiri ya yi a wasu jihohin da ake samun waɗannan damuwoyi.

A Jihar Filato, shirin ya gamu da matsaloli na rashin fara gudanarwa akan lokaci. Don haka babu wani kyakkyawan tsari na iya tunkarar ƙalubalen da ya taso, kuma ga ƙarancin kuɗaɗen da za a gudanar da aikin kewaye wasu makarantu da suke a buɗe. Sannan suna ƙoƙarin haɗa kai da hukumar ‘yan sanda, da ta NSCDC, da ƙungiyoyin tsaro na ‘yan banga, domin taimakawa wajen tsaron makarantun kwana da ake da su a ƙauyuka da wasu ƙananan hukumomin jihar, yayin da ake duba yiwuwar mayar da wasu makarantun zuwa na jeka-ka-dawo. Abin da ya kamata sauran jihohi masu su yi koyi da wannan tsari, ko su fitar da wasu tsare-tsare na daban da suka dace da yanayin da jihar su ke ciki.

Wata muhimmiyar shawara kuma shi ne, ƙarfafawa da kuma kafa majalisar haɗin gwiwa tsakanin al’ummar yankin da makaranta take, ƙungiyar malamai da iyayen yara ta PTA, ƙungiyar tsofaffin ɗalibai, da sauran masu faɗa a ji na cikin al’umma, wanda a taƙaice ake yi wa laƙabi da SBMC, domin a tabbatar da ganin an taimaka da shawarwari da kuɗaɗen gudanar da tsare-tsaren da suka kamata don inganta tsaro a makarantun da yaranmu suke.

Ba zai yiwu mu naɗe hannu muna jiran sai gwamnati ce za ta samar da tsaron makarantun da muke da su ba, wannan ƙalubale ne mai girma, wanda dole sai mun sa hannu. Mu haɗa kai da shugabannin makarantu, jami’an tsaro da gwamnati, don mu ga wacce gudanarwa za mu bayar wajen ƙarfafa gwiwar jami’an tsaro, a samu kula da mu da yaranmu. Wannan matsala ce mai girma, kuma gwamnati ita kaɗai ba za ta iya ba.

Allah Ya taimake mu akan wannan kyakkyawar niyya ta mu, Ya ba mu ikon samun galaba kan matsalolin da suke neman fin ƙarfin mu.

By ukarofi