Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Kamar yadda wasu magoya bayan Isra’ila a Najeriya ke kawar da kai kan kisan gillar da ake yi wa Musulmi da Kiristoci a Gaza don a wajen su Isra’ila ba ta laifi, haka ne karara ‘yan ikirarin Hausa zalla su ka kau da kai ga mulkin mallakar Turawa da bautar da kakakanni da su ka yi, su ka dukufa haikan wajen zagin Mujaddadi Shehu ɗanfodiyo. Mujaddadi na Musulunci ma ya koma ga Allah kimanin shekaru 86 kafin ‘yan mulkin mallaka su zo don haka shi bai ma gamu da ko ɗaya daga masu jajayen kunne da su ka shigo da addinin Kirista ba. Shehu ya koma ga Allah ya bar al’ummarsa cifcif ba wani ƙabilanci. Kuma tabbas da Turawan su ka zo sun samu jama’ar Shehu a haɗe su ka koma kuma su ka bar su a cikin addininsu!. Don haka duk waɗanda a yau ke zagin Shehu dama can ba su amsa kiran sa ba ne ko kuma su na kan iyaka; ko su yi nan ko su yi can, duk inda ta samu shikenan, in ta yi ruwa rijiya in ta ki ruwa masai. Sam-sam na maimaita ba Musulmi da ke zagin Shehu.
Duk mai inkarin wannan bayanin ya sayi fili a kowane gidan rediyo a da’irar Arewa kasar Shehu ya yi bayanansa da ya ke yi a soshiyal midiya sai ya buƙaci a buɗe layi mutane su bugo waya don faɗar albarkacin baki, zai gane shayi ruwa ne. Mun tabbatar makirci ne da a ke rurutawa don akasarin masu kamfen din nan a ɓoye su ke ƙirib a wayar salula a tunaninsu na rashin sanin kimiyyar na’ura, ba sunan gaskiya ba hoto su na aibata manyan jagororin da akasarin jama’a ke mutuntawa.
Wannan kwangilar ba ta da wani riba hatta ga masu yin ta in ka debe more alƙalamin son zuciya da abun duniya da su ke samu; amma in wutar ta kama bal-bal za ta rutsa da kowa kuma in ma wasunsu ‘yan kalilan na makale a waje ko gefen Daular Shehu, akwai danginsu ko ‘yan addininsu. In haka ne ina amfanin badi ba rai. Gaskiyar magana duk wutar da za ta kama Arewa fa sai ta lashe Nijeriya kakaf.
Ganin mutum ɗan kwangilar rusa Arewa ya yi rubuta a yanar gizo wasu abokan burminsa na taya shi, ba shi ne asalin abun da ya ke a kasa a kokuwar Arewa ba. Ni ba na ma jan hankalin masu cewa za su kwace gidajen sarauta, don duk mai buƙata ga gidajen nan ya shiga ya gwada ma na. Ba ma haka ba ko gwamnatocin siyasa ba da hauka su ke taba gidajen sarauta ba. Mai hankali ya duba hagu da dama, yanayin nan na Arewa ga mu dai da ke raye yanzu, haka za mu koma ga Allah mu bar yankin. Abun addu’armu na bayanmu su dora alheri kar su kaucewa tarbiyya da tarihin gaskiya na Lardin.
Juya kamfen zuwa ƙabilanci ba dai a nan Arewa ba. Duk mai wannan ha’inci za ka taras ɗan karamar ƙabila ce ko gyauron waɗanda ba su rabauta da kiran Shehu ba. Arewa ta wuce wani ya kawo ƙabilanci ya keta haddin yankin musamman da fakewa da harshen Hausa mai daraja. Duk mai ƙabilanci ya tafi kauyensu ya yi ta fama da ‘yan ƙabilarsa. Mun haska da yawa daga ‘yan basaja masu shigar burtu da nuna Hausawa ne alhali ba su da alaka ta kusa ko ta nesa da Hausa. Mun yi ƙalubale ga waɗanda su ka fi zakewa su fito fili a gan su don tabbatar da iƙirarin su amma tsit ka ke ji, yo hauka su ke yi ka na nan ɗan banza bakwai na zamanin yau ka fito a gan ka daga mutanen can da kan tare hanya su na kashe matafiya don kiyayyar bambancin addini? Wallahi sun sha kashe matafiya kuma har yanzu ba su daina ba don haka su ka ɗinka rigar Hausawa a soshiyal midiya don hallaka Arewa. Shin bature ma mai kera AK 47 bai iya murkushe ruhin Daula ba balle baleri mai naɗe hannu!
A nan ina son amfani da wannan dama wajen nanata yabo ga matasanmu masu basira da ke daurewa su na ankarar da waɗanda ba su san dawar garin ba da kan tsinci miyagun maganganu a yanr gizo don su gane takun ‘yan kwangila da yin watsi da su. Duk wasu zayyane-zayyane da zane-zane na karyar neman ‘yanci daga ‘yan kwangilar nan, a yi wancakali da su. Al’ummar Arewa daya ce kuma kowa na da ‘yancin neman duk alheri da mukami da ya ke so a Lardin. Tsarin mulkin Nijeriya na 1999 (gyararre) mu ke amfani da shi. A cikinsa akwai ‘yanci ga dukkan ‘yan kasa ta fannin addini, mu’amala, zamantakewa da sauransu. Duk mai faɗin wani abu na an danne wani, to mai neman tada tarzoma da yakin basasa ne.
Mu gujewa mugayen mutane irin su Ouba Ali Mohaman na Kamaru mai cillo harshen wuta Nijeriya don ta wargaje, alhali ya na yayyafa ruwan sanyi a kamaru don kwantar da masu rajin kafa Ambazonia. Hakanan ga wani mugun Bayarbe Kayode Salman Banjo mai ruruta wutar fitina da karyar son Hausawa. Ya kamata Hausawa su taka ma sa birki don annamimi ne maƙiyin Hausa da Hausawa. Ga ‘yan IPOB masu ingiza ‘yan kwangila su tada fitina a Arewa don hakan ya ba su damar sauƙin ballewa don kafa ƙasar ‘yan awaren Biyafara. Kun ga in Arewa ta birkice ai ba mai takawa Biyafara birki kamar yadda dakarun Arewa su ka yi a 1967 har Ojukwu ya arce daga ƙasar. Ga Nnamdi Kanu a gidan yari ya na girbar muguwar rawa da ya taka.
Na ga wasu na kawo bayanan da su ke cewa na tarihi ne inda akwai waɗanda su ka zaƙulo daga rubuce-rubucen maƙiya Shehu sai wadanda su ka turo rubutu ba ma wanda ya rubuta na asali. Haba yaya za a yi ka kawo rubutu daga waɗanda sam ba su san darajar Islama ba balle yadda a ke gudanarda harkokin Islama ya zama hujja. Shin ba ku ga masu kamfen ɗin haddi na Musulunci ma kauyanci ba ne lallai a rushe shi. Kai akwai masu ganin me ya sa ma za a yi alwala gabanin sallah maimakon tun da mutum ya yi wanka ya shafa mai ya auka masallaci ya yi sallarsa. Haƙiƙa duk wanda bai san Musulunci na aiki ne bisa umurni da dokoki ba fiye da ɗan cikin cokalin hankalin dan-adam; zai iya yanke hukunci ko biyewa ‘yan duniya hayakin taɓa su rubta shi a ƙarerayin murde tarihi da su ke yaɗawa. Mu dai ba wani mai son zuciya da zai kawo ma na tatsuniya mu biye ma sa.
Hatta kan jihadin da manzon Allah ya jagoranta, waɗanda ba imani ba kan ce yaya za a yi a taya Allah yaƙi tun da ya na da ikon komai a kyale shi ya yaƙi waɗanda su ka bijirewa dokokinsa!. Jihadin da Shehu Usmanu ya yi na jaddada Musulunci ne shi ya sa a ke yi ma sa laƙabi da mujaddadi. Kun ga wasu masu suka na cewa wai Shehu ya yi jihadi a kan musulmi alhali ba su san cewa a kan yi jihadin a kan musulmin da ya zama munafuki da nassin Alkur’ani. Allah madaukakin Sarki ya bambance tsakanin kafurai da munafukai kuma duk ya yi umurni a yake su, TAWBA 73. Balle ma ka je ga masu shirka, matsafa da sauran su. Hasalima Shehu wa’azi ya riƙa yi har sai da ta kai a ka yi yunƙurin yi ma sa kisan gilla da tsangama iri-iri amma masu suka ba sa ambata wannan tarihin.
Kammalawa
Duk waɗanda su ka rubuta tarihin da ba daidai ba na Shehu za ka ga ‘yan amshin shatan Turawan mulkin mallaka ne wadanda su ka yi iya makircinsu don canjawa al’ummarmu tsarin rayuwa su ka kasa. Idan ka yaƙi mutum a kan gaskiyar sa ka kasa nasara to dayan biyu; in ma ka maida faɗan wasa ko ka juya zuwa sharri ko shafa bakin fenti. Hakika abun da ya faru kenan, kama daga wadanda ke cusa ƙabilanci a aikin Shehu ko ma su kawo labarun shirme na an kai hari kan malaman ‘Yandoto, an kai hari Zazzau Sarki Makau ya na masallacin idi. Masu suka iya nan su ka fi maƙalewa kuma duk tushen rubutun daga makiya Shehu ne waɗanda su ka so kowa ya bi tsarin da su ke bi. Tun da mun ƙi bin na su sai su ka ɗau ‘yan kwangilar ruruta fitina a cikin kasarmu su ka horar da su hanyoyin da za su rikitawa mutane kwakwalwa don cusa shakku da shubuha da zai kai ga har mutum zai yi nadamar yanda iyayensa ma su ka haife shi a cikin addini.
Ai an fara biyowa ta nuna babu ma Allah ba Annabin Allah, wato a sa mutum ya kafurce ya koma biyewa addinin tunaninsa ATHEISM. Tsakani da Allah ba mu ga wasu ‘ya’yan Musulmi da su ka ayyana cewa su masu akidar ba Allah ba ne?. Rashin nasarar wannan kamfen ɗin ya kawo wannan sabuwar loga ta shigar burtu da wasu masu ha’inci ke yi da dinka rigar Hausawa wai su a dole su na kwatawa Hausawa ‘yanci ne. Mu ƙaddara ma maganar su gaskiya ce, me ya sa su ka ɓoye kan su ba hoton gaskiya ga sunan karya? Yaya za a yi matsoraci ya kare Hausawa? Zama lafiya ya fi zama ɗan Sarki.
