Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Mutane sun shiga firgici da ɗimuwa a safiyar jiya Alhamis, 11 ga Disamba, 2025, bayan hatsarin mota mai tsanani da ya yi ajalin ɗaliban Jami’ar Jos (UNIJOS) takwas tare da direban motarsu akan titin Zariya da yake cikin garin Jos, Babban Birnin Jihar Filato.
Shaidu sun ce, hatsarin ya faru ne a lokacin da wata babbar mota ƙirar tirela, wacce ake zaton ta samu matsalar birki, ta ƙwace wa direban ta bugi ɗaya daga cikin motoci biyu da ɗaliban suka ɗauka, domin zuwa yawon dare. Sai bugun ya fasa motar gabaɗaya tare da jefa ta kai tsaye kan sandar wutar lantarki kusa da gadar Farin Gada.
A cewar shaidun, ɗalibai biyu sun tsira, amma an garzaya da su asibiti cikin gaggawa, saboda munin raunukan da suka samu.
Wani daga cikin waɗanda suka tsira ya bayyana irin tashin hankalin da suka shiga, inda ya ce, “bugun ya fasa motar kaf-kaf ya kashe mutane takwas nan take. Mu da muke baya, ƙarfin bugun bai kai gare mu sosai ba. Bayan tirela ta ƙwace ta buge mu, nan take motar ta fara karkacewa kafin ta buge sandar lantarki. Dukkan abin ya faru cikin ’yan daƙiƙu kaɗan ne.”
Rahotanni sun nuna cewa, ɗaliban suna kan hanyarsu ta koma wa mazauninsu ne bayan yawon dare da suka yi da misalin ƙarfe biyu na dare lokacin da hatsarin ya afku.
Jaridar Daily Post ta ruwaito cewa, Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Filato, DSP Alabo Alfred, bai samu damar tabbatar da lamarin ba a lokacin haɗa rahoton nan, amma wani jami’in ’yan sanda ya tabbatar cewa, an fara farautar direban tirelar, wanda ya tsere daga wurin bayan afkuwar hatsarin.
Masana harkar sufuri da hukumomin tsaro sun daɗe suna jan hankalin direbobi kan matsalolin gudu fiye da ƙima da tuƙi cikin maye, waɗanda ake ganin suna daga manyan ɗalilan yawaitar irin waɗannan hatsurra a faɗin ƙasar nan bakiɗaya.
