Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
“Ƙananan hukumomin Jihar Katsina yanzu sun shafe fiye da Watanni shida suna cikin zaman lafiya ba tare da katsewa ba.
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Raɗɗa ya bayyana ingantacciyar ci gaban tsaro da wasu ƙananan hukumomi, musamman waɗanda a da suke fama da hare-haren ‘yan bindiga akai-akai.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake karɓar sabon kwamandan 213 Forward Operating Base (FOB), Katsina, Air Commodore Chukwuedo Illoh, a Fadar Gwamnati, Katsina.
Air Commodore Illoh, wanda ya fito daga Regular Course 45 na Nigerian Defence Academy, ya zo da gogewar aikin soja na sama da shekaru 30. Ya riƙe wasu muhimman muƙaman jagoranci kuma ya taɓa zama Defence Attaché na Najeriya a Paris, tare da ƙarin wakilci zuwa ƙasashe 13 na turai.
Air Commodore Illoh shi ne Air Component Commander na Operation FANSAN YAMMA, kuma ana sa ran zai jagoranci dukkan ɓangaren sojin sama na Joint Task Force (North-West).
A jawabin sa, Gwamna Raɗɗa ya jaddada cewa ayyukan ‘yan bindiga sun ragu matuƙa, musamman a wasu manyan yankuna da suka kasance mashahuran cibiyoyin hare-hare.
“Yanzu haka kusan dukkan ƙananan hukumomin da abin ya shafa sun cimma yarjejeniyar zaman lafiya da ‘yan bindiga, kuma a wurare da dama mun shafe dogon lokaci ba tare da hare-hare ba,”Dikko ya ce.
“Jibia ta kasance ɗaya daga cikin wuraren da suka fi hadari, amma yanzu kusan watanni shida kenan ba a samu ko hari ɗaya ba. Batsari, Safana da Ɗanmusa ma sun shafe kusan watanni biyar zuwa shida ba tare da wani lamari ba,” inji Gwamna Radda.
Ya ƙara da cewa duk da cewa wasu ‘yan bindiga sun yi yunƙurin matsawa zuwa kudancin jihar, rundunonin tsaro sun ɗauki matakin gaggawa cikin nasara.
“Da farko wasu yankuna na jihar su ne manyan mashahuran hare-hare. Daga baya lamarin ya fara yaɗuwa zuwa makwabtansu, amma alhamdulillah ƙoƙarinmu ya amfana, kuma muna ƙoƙarin ganin zaman lafiya ya ɗore,”inji gwamnan.
Yayi fatan ayyukan sintiri za su ƙara inganta zaman lafiya a jihar.
Da yake tunawa da halin da ya tarar da shi lokacin da ya hau mulki, gwamnan ya ce ƙananan hukumomi 24 na fama da barazana mai tsanani. A cikin watanni biyar na farko, ya kafa Katsina State Community Watch Corps domin ƙarfafa tsarin tsaro gaba ɗaya.
“Ba za ka iya yaƙi irin wannan rikici ba tare da mutanen ƙauyuka ba. Mun ɗauki maza daga yankunan da abin ya shafa. Suna sanin yankunansu, suna ba da bayanan sirri, kuma suna da ra’ayin ganin a kawo ƙarshen matsalar saboda iyalansu na cikin haɗari.”Dikko ya ce.
Ya ce hadin gwiwar da aka samu tsakanin Sojin Sama, Sojin Kasa, ‘Yan Sanda, Civil Defence da Community Watch Corps ya tilasta wa wasu ƙungiyoyin ‘yan bindiga neman sulhu a ƙarƙashin tsauraran sharuɗɗa.
Gwamna Raɗɗa ya kuma yaba da rawar da rundunar sojin sama ta taka.
‘Yan bindiga suna tsoron hare-haren sama fiye da komai, kuma ɓangaren sojin sama ya taka rawar gani wajen raunana su. Magabatan ka sun kafa Rapid Response Squad na sansanin, wanda shi ma ya taimaka wajen samun ci gaban da aka yi.
Gwamnan yayi alƙawarin ci gaba da tallafa wa sojojin sama da duk abin da suke buƙata don aiwatar da ayyukansu cikin nasara,” inji shi.
A farkon jawabin sa, Air Commodore Illoh ya ce:
“Na shaida da kaina irin gagarumin ƙoƙarin da kuke yi wajen kawar da ‘yan bindiga da duk wani nau’in laifi a Jihar Katsina.”
Ya ci gaba da cewa:
“Ba za mu iya magana game da tsaro a jihar ba tare da ambaton jagoranci ba. Tsaro haƙƙi ne na kowa, amma jagoranci dole ne ya fito daga wani wuri, kuma kun nuna hakan a fili.”
