DSS ta sako mutane uku da biyan su diyyar miliyan N3 bayan tsare su kan zargin hannu a garkuwa bisa kure

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Tsaro ta farin kaya DSS, ta sako mutane uku da aka kama su bisa kuskure kuma aka tsare su bisa zargin su da hannun a ayyukan garkuwa da mutane da fashi, bayan bincike ya nuna ba su da hannu a wani mugun aiki.

Mutanen sune; Umar Ibrahim, Alhaji Bello Rabiu, da Jaja Sarki Bamo, waɗanda suka kasance a hannun hukumar tun watan Yunin 2025 a lokacin da jami’an DSS suka kama su a Filin jiragen sama na Tunde Idiagbon jim-kaɗan bayan dawowarsu daga aikin hajji.

An zarge su ne da hannun a alaƙa da ayyukan garkuwa da mutane, wanda daga bisani aka gano cewa babu ƙamshin gaskiya acikin sa.

Wani babban jami’in DSS ya shaida wa manema a yau Juma’a cewa tabbas an sako mutanen, sannan an biya su tarar Naira miliyan 3 domin gyara ga kuren.

A ƴan watannin nan hukumar tana sako mutane bayan binciken ya nuna ba su da hannu akan abinda ake tuhumar su a kai, lamarin da ya sa aka gano an tsare da dama ba bisa haƙƙi ba.

Wani jami’i da ya nemi a sakaye sunansa ya bayyana cewa hukumar ta sake salo ne ƙarƙashin jagorancin Darakta Janar Adeola Ajayi, wanda ya tsaya tsayin daka wajen tabbatar da gaskiya da adalci ta hanyar bin hanyoyin da doka ta tsara wajen yi dukkan wanda ya shigo hannun hukumar adalci.

Tuni waɗanda aka sakon suka nuna godiya ga jagorancin DSS da yadda suak kula da su bisa mutuntawa yayin da ake tsare da su.

By Babaji