Zargin rashawa: An tsare tsohon Ministan Ƙwadago, Chris Ngige a Kurkukun Kuje

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mai Shari’a Mariam Hassan ta Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci a tsare tsohon Ministan Ƙwadago da Ɗaukar Aiki, Chris Ngige a gidan gyaran hali na Kuje.

An ruwaito cewa, an tsare Ngige ne bisa tuhumar sa da hannu a rashawa, wanda zai cigaba da zama a gidan hat zuwa ranar Litinin inda za a saurari ƙorafin neman belinsa.

Musamman ana tuhumar tsohon ministan ne da laifin bada kwangilolin ayyuka da dama ba bisa ƙa’ida ba a lokacin da yake minista tsakanin shekarar 2015 zuwa 2023.

Haka kuma, an zarge shi da karɓar miliyoyin nairori daga ƙungiyoyi yayin da yake ofis.

Saidai duk da haka, Ngige ya musanta baki ɗaya tuhume-tuhume takwas da EFCC ta gabatar akansa.

Mai ba shi kariya, Patrick Ikweato (SAN) ya roƙi kotun da ta bada damar kuka da lafiyar Ngige har zuwa lokacin sauraron bada belin nasa.

Da take hukunci akan al’amarin, Alƙali Mariam Hassan ta ɗage shari’ar zuwa ranar 15 ga watan Disamba.

By Babaji